Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Kunar bakin Wake ya kashe Soja daya da Dan banga a Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta samu rahoto da cewa wasu ‘yan matan Boko Haram biyu sun fashe da Bam a yayin da suke kokarin isa wata shiyya a kauyan Monguno.

Wannan abin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabatar, bisa rahoton da aka isar ga Naija News, da cewa Mutum aka kashe sakamakon tashin Bam din, Watau Soja guda da dan banga daya.

An bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan ta’addan sun fashe kansu da bam ne a yayin da suke kokarin guduwa bayan da Jami’an tsaro ke kokarin tsayar da su don bincike a hanyar da ta bi mafitar kauyan Monguno.

“Mun rasa Soja daya da wani dan banga a fashewar bam din. daya daga cikin jami’an tsaron mu kuma yayi mugun raunuka” inji bayanin da wani Soja da bai bayyana sunansa ba ya bayar ga manema labarai.

Don karin bayani game da lamarin, wani soja ya kara da cewa daya daga cikin ‘yan ta’addan, da ta gane da cewa jami’an tsaro na neman gane likin su, sai tayi wuf ta ari na zomo. “Da Sojojin suka gane da hakan sai suka bi sauran da gudu, ana cikin hakan ne ‘yar macce gudan kuma da ke sanye da bam sai ta tayar da bam din a nan take ta mutu hade da jami’an tsaro biyun.” inji shi.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Daraktan yada labarai ga rundunar sojoji, Col Sagir Musa ya gabatar da cewa rundunar sun yi ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a yankin Maikadiri, bayan wata kirar gaugawa da suka karba daga ‘yan bangan yankin da cewa sun gane da motsin ‘yan ta’adda a kan hanyar yankin.