Gwamna Ganduje Ya Nada Mata Mataimaka na Musamman Guda 5 A Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya gabatar da nadin wasu mata Biyar a Kano

Wata tsohuwar Kwamishina mai kula da harkokin mata, Hajiya Hajiya Yardada Maikano Bichi, tana daga cikin mata biyar na Musamman Mataimaka, wadanda gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nada.

Gwamna Ganduje bayan nadin dukkansu da kuma bayar da umarnin su fara aiki nan take, ya umarci dukkan wadanda aka nada da su tabbatar da kwarewarsu yayin aiwatar da ayukansu a kowane ofishi.

A cewarsa, “tunda aka zabe ku a cikin jerin mutane da yawa, ya nuna a fili da cewa muna tabbatar wa jihar da cewa kuna da abin da zai kawo ci gaban jihar.”

“Ya kamata ku tabbatar da cewa kun bi dukkanin manufofin gwamnati da shirye-shiryen da suka danganci ofisoshinku, har ma da hakan, kuna kulawa da su da dukkan hankali.”

Wadanda aka nada sun hada da, Hajiya Fatima Abdullahi Dala, a matsayin mai ba da shawara ta musamman a shafin Kulawa ga Yara da kuma Ayukan Mata; Dokta Fauziyya Buba a matsayin mai ba da shawara ta musamman a Ma’aikatar Kiwon Lafiya; Hajiya Aishatu Jaafaru, mai ba da shawara ta musamman kan Shirin ciyar da ‘yan makaranta;  Hajiya Hama Ali Aware kuma a matsayin Mai Bada shawara na musamman akan Zuba Jarin Kasashen waje, da kuma Hajiya Yardada Maikano Bichi, a matsayin Mashawarci na Musamman kan Kungiyoyi masu zaman kansu.

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Ranar Da Zata Fara Biyan Mafi Karancin Albashi Na N30,000

Ma’aikata a jihar Kano zasu shiga cikin murmushi da jin daɗin a yayin da gwamnatin Jihar zata fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N30,000, in ji gwamnatin jihar.

Wannan ya biyo ne bayan kammala tattaunawar nasara tsakanin gwamnatin jihar da majalisar hadin gwiwar  ma’aikata a jihar ranar Alhamis.

A cewar wasikar da ke isar da ci gaban, za a aiwatar da biyan kudin ne daga watan Disamba na 2019 yayin da za a yanke hukunci kan wasu kudaden.

Sakon na kamar haka;

“Gwamnatin jihar Kano ta amince da fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata daga watan Disamba 2019, a yayin da kuma za a fara biyan albashin watan Afrilu-Nuwamba 2019.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Afrilu ta shekarar 2019, ya sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi a cikin doka, da kuma bayar da dama ga gwamnatocin jihohi da shugabannin kwadago a jihohinsu don aiwatar da ayukansu a dayance.

This online medium recalls President Muhammadu Buhari had in April 2019, signed the new Minimum Wage Act into law paving way for further negotiations between the state governments and the labour leaders in their respective states.

Gwamnan Kano Ya Haramta Daukar Macce Da Namiji Cikin Keke Napep Daya

Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa shigar namiji da macce a cikin ‘Keke Napep’ guda a fadin jihar daga watan Janairu, 2020.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a bikin rufe taron shekara da shekara karo na 77 da kungiyar shirya hutu ta Musulunci (IVC) wanda Zone A na kungiyar ‘Muslim Society of Nigeria (MSSN)’ ta gudanar a Jami’ar Bayero, Kano.

Naija News Hausa ta fahimci cewa a taron wanda Kwamandan Hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya wakilci Gwamna Ganduje, ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar kiyaye martabar addinin Musulunci ne.

Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ne ya fara gabatar da tsarin ‘Keke Napep’ wanda aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ don daukan mata kawai a Kano tun farko a lokacin da yake shugabancin jihar.

Wannan ya biyo ne bayan da gwamnatin Shekarau ta haramtawa ‘yan kabukabu da daukar mata.

Amma tun bayan ficewar tsohon gwamna, Shekarau,  an bayar da damar ci gaba da daukar mutane daga dukkan jinsi, watau macce da namiji a shiga guda, wanda a haka gwamnatin jihar ta yi yunkurin canza yanayin.

A wajen hidimar, Gwamna Ganduje ya kuma gargadi mahalarta da su fuskanci karatun su da kuma kaurace wa shan kwayoyi.

Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Ya Karbi Nadin Da Gwamna Ganduje Yayi Masa

Rahoton da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa Mai martaba Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya ba da sanarwar amince da nadin nasa a matsayin shugaban majalisar masarautar jihar Kano.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya baiwa mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido, kwana biyu don bayyana ra’ayinsa da mukamin da aka bashi ko kuma ya tsige shi daga kujerar sarauta.

A yau 20 ga Disamba 2019, Mataimakin gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi kira da suna Dawisu ya sanar da tabbaci da cewa sarki Sanusi ya amince da nadin da aka yi masa.

Sakon wadda aka wallafa a shafin yanar gizon zumunta na Twitter na kamar haka;

“Mai martabar, Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, a yau, ya amince da nadin nasa da H.E @GovUmarGanduje ya yi a matsayin Shugaban Majalisar Masarautar Kano, wanda ya kunshi dukkan masarautuka 5 a jihar da sauran membobi.”

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Najeriya Ba Za Su Sake Barci Ba Da Sun San Abin Da Ke Gudana a Kasar – TY Danjuma

Ganduje Ya Baiwa Sarki Sanusi Kwana Biyu Don Daukan Wasu Matakai Ko Ya Tsige Shi

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya baiwa mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido, kwana biyu don karba ko kin amincewa da nadin nasa.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano ya nada Sanusi a matsayin Shugaban Majalisar Masarautar Kano.

‘Yan kwanaki bayan nadin da gwamnatin Ganduje ta nada, Mai Martaba Sarkin Kano ya ki sanar da gwamnatin jihar game da yarda ko kin amincewa da nadin.

Gwamna Ganduje a cikin wata sanarwa da aka bayar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana zancen baiwa sarki Sanusi kwana biyu kawai don bayyana ra’ayinsa.

Sakon na kamar haka;

“Gwamnatin jihar Kano ta bayar wa Mai martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido, kwana biyu kacal don sanar da gwamnatin jihar da ra’ayinsa kan amince ko rashin amincewa da matsayin da aka bashi na zaman Shugaban Majalisar Masarautar Kano.”

Ku tuna kamar yadda Naija News Hausa ta sanar a baya, cewa Babbar kotun jihar Kano ta baiwa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ganduje ikon cire duk wani sarki a cikin a bisa tsarin doka.

Mai shari’a A. T. Badamasi wanda ya sanar da haka a Kotu bayan ya ki bayar da damar tsawaita karar umarnin  hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar kutsa kai da kuma iko kan masarautar Kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje Yayi Wasu Sabbin Nadin Mukami a Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin sabbin shugabannan ma’aikata da masu ba da shawara na musamman.

Gwamnan ya amince da nadin Hajiya Binta Lawan Ahmed a matsayin shugabar Ma’aikata wacce za ta maye gurbin Dr Kabiru Shehu, wanda ya kasance mai rikon kwarya ga mukamin, tun bayan kammala shekarun sa tare da ma’aikatan gwamnatin jihar, makonni kadan da suka gabata.

Har zuwa lokacin da aka nada ta, Hajia Ahmed ita ce Sakatariyar Ma’aikatar Kasuwanci ta dindindin a jihar.

Sanarwan nadin ya fito ne a kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai ga gwamnan jihar Kano, Abba Anwar.

Sanarwar ta ce, Gwamnan ya bayyana sabon Shugaban Ma’aikata din a matsayin ma’aikaciyar gwamnati mai sadaukarwa, wanda “a koyaushe tana tabbatar da kwarewanta a matsayinta na ingatacciyar ma’aikaciyan gwamnati, wadda niyyarta ita ce ganin ci gaban ma’aikatar jihar.”

Gwamnan ya kuma yaba wa Dakta Shehu kan kyakkyawan ayyukan da ya yi a jihar, tare da lura cewa “Dr Kabiru Shehu ya taka rawar gani sosai. Ya kasance Shugaban Ma’aikata mai hali na gari da hulda da jama’a. Duk muna yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.”

A haka gwamna Ganduje ya kuma amince da nadin wasu mashawarta na musamman.

Duba cikakken jerin sunayansu da mukaminsu a kasa:

1- Ali Baba (A Gama Lafiya)  – Mashawarci na Musamman, Harkokin Addini

2- Mustapha Hamza Buhari (Ba-Kwana) – Mai ba da shawara na musamman kan Harkokin siyasa

3. Hamza Usman Darma –  Mai ba da shawara ta musanman akan Ayyuka na Musamman

4. Tijjani Mailafiya Sanka – Mashawarci na Musamman a Majalisar Masarauta

5. Yusuf Aliyu Tumfafi –  Mai ba da shawara na musamman kan Manyan Ayuka

Gwamnan ya caje su da jajircewa wajen aiwatar da ayukansu da tabbatar da yin aiki don ci gaban jihar.

“Ina fatan za ku yi aiki tukuru domin daukar jiharmu zuwa matakin gaba. Kamar yadda kuka san cewa, kun dace dukanku da ofishin da aka sanyaku,” inji Ganduje.

Babbar Kotun Jihar Kano Ta Baiwa Ganduje Iko Kan Masarautar Jihar

Babbar kotun jihar Kano ta amince da baiwa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ganduje ikon cire duk wani sarki a cikin a bisa tsarin doka.

Mai shari’a A. T. Badamasi wanda ya sanar da haka a yau a Kotu bayan ya ki bayar da damar tsawaita karar umarnin  hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar kutsa kai da kuma iko kan masarautar Kano.

Naija News Hausa ta fahimci cewa alkali da kuma mai ba da shawara ga masarautar a cikin kara mai lamba K/197/2019 ya roki kotun da ta ba da umarni tsawaita hana damar ga Ganduje har sai an cimma karshen sauraren karar.

Amma bisa ga hukuncin yau zai zama da cewa gwamna Ganduje a yanzu yana da damar yin amfani da dukkan ikon da yake da shi a ƙarƙashin sabuwar dokar Majalisar Masarautar Kano ta 2019.

Kotu Ta Ba Da Hukuncin Karshe Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa Ga Gwamna Ganduje

Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yi watsi da wata kara da wani lauya a Kano, Bulama Bukarti ya shigar a gabanta na neman umarnin kotun da ta tilasta wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati (EFCC) don ta binciki gwamna Abdullahi Ganduje bisa zargin karbar cin hancin daga hannun wani dan kwangila.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, arewacin Najeriya, ta yi watsi da karar a ranar Litinin da yamma, 16 ga Disamba saboda “rashin hujja”.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi a jihar Kano, Arewacin Najeriya, ya kori Shugabannin Gundumomi guda biyar a yankin nasa.

An bayyana da cewa matakin Alhaji Aminu kan cire Shugabannin Gundumomi biyar din ya faru ne saboda rashin biyayya ga Sarki Aminu Ado Bayero da masarauta bi da bi.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 17 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 17 ga Watan Disamba, 2019

1. Rundunar Sojojin Najeriya Sun Sarwake Major Janar 20, Brigadier Janar 10

Rundunar Sojojin Najeriya sun sake girke Manjo-janar 20 da Birgediya-Janar 10 a cikin abin da ake gani a zaman babban koma-baya a rundunar.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Sojojin Najeriya sun ba da sanarwar sake daukar manyan hafsoshin sojojin ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, 16 ga Disamba ta hannun Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kanal Sagir Musa.

2. Boko Haram: Leah Sharibu Ta Saura Da Rai – Bisa Bayanin Malamin Jami’a Da Aka Sace

Wani Malamin Jami’ar wata kwaleji da wasu mutane goma wadanda kwanan nan ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace su, sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da su daukin matakin ceton su daga hannun ‘yan ta’addan.

Wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan kisan wasu ma’aikatan agaji hudu da kungiyar Boko Haram ta yi. ‘Yan ta’addan sun sace ma’aikatan agajin ne da a baya aka kashe a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

3. Kotu ta Ba da hukuncin Karshe akan Gwamna Ganduje Kan Cin Hanci Da Rashawa

Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yi watsi da wata kara da wani lauya a Kano, Bulama Bukarti ya shigar a gabanta na neman umarnin kotun da ta tilasta wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati (EFCC) don ta binciki gwamna Abdullahi Ganduje bisa zargin karbar cin hancin daga hannun wani dan kwangila.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, arewacin Najeriya, ta yi watsi da karar a ranar Litinin da yamma, 16 ga Disamba saboda “rashin hujja”.

4. Dalilin da yasa DSS baza ta iya sakin Omoyele Sowore ba – Malami

Babban Lauyan Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce ba zai iya ba da umarni ga ma’aikatar ta DSS ba don su saki Omoyele Sowore.

Malami ya fadi hakan ne don mayar da martani ga kiran kalubalai da lauya da kuma mai ba da shawara ga Sowore, Femi Falana (SAN), ya bayar na neman shi da ya umarci ‘yan sanda asirin da su saki Sowore.

5. APC Ta Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Akeredolu, Okorocha da Sauransu

Shugabannin jam’iyyar APC ta kasa baki daya a ranar Litinin sun dage dakatarwar a kan Gwamna Rotimi Akeredolu, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Rochas Okorocha, Mista Osita Okechukwu, da Fasto Usani Uguru Usani.

Jam’iyya mai mulki ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, wace kuma ta aika wa kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta hannun Sakataren yada labarai na kasa ga Jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu.

6. Sarkin Bichi Na Jihar Kano Ya Tsige Hakimai 5

Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi a jihar Kano, Arewacin Najeriya, ya kori Shugabannin Gundumomi guda biyar a yankin nasa.

Naija News ta samu labarin cewa an cire Shugabannin Gundumomi biyar ne saboda rashin biyayya ga Sarki Aminu Ado Bayero da masarauta bi da bi.

7. Wata Rukuni Na Zargi Fayemi da yin Makirci don maye gurbin Osinbajo da Tsige Oshiomhole

Bangaren yada labarai ta Jam’iyyar PDP a reshen jihar Ekiti, ta zargi gwamna Kayode Fayemi da shirya makarkashiyar maye gurbin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Litinin ta hannun Bola Agboola, kungiyar ta nemi tsohon Ministan da ya daina shirin tsige Shugaban Jam’iyyar na kasa baki daya, Adams Oshiomhole.

8. Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.

Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 11 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 11 ga Watan Disamba, 2019

1. Kasar UK Ta Aika da Sako Mai Karfi Ga Shugaba Buhari Tsare Sowore

Kasar Burtaniya (Burtaniya) tayi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta mutunta bin doka da sakin Omoyele Sowore, mai jagorar zanga-zangar #RevolutionNow.

Kamfanin dilanci na Naija News ta ba da rahoton cewa Burtaniya ta yi wannan kiran ne a shafin yanar gizo, watau twitter, a ranar Talata, 10 ga Disamba, don tunawa da “Ranar Kare Hakkin Bil-Adama.”

2. Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Matakin Ganduje Na Kira Sabbin Masarauta A Kano

Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da Gwamna Abdullahi Ganduje daga kirkirar sabbin masarautu ba tare da tuntuɓar masarautar Kano ba.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, wasu masu nadin sarauta a karkashin jagorancin Yusuf Nabahani, Madakin Kano, sun nemi kotu ta bayar da umarnin dakatar da gwamnan daga matakansa.

3. Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Nadin Sabon Ciyaman Na AMCON

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Edward Adamu a matsayin Shugaban Kamfanin Kula da Bada da Talla na Najeriya, watau ‘Asset Management Corporation of Nigeria’.

Kamfanin Dilancin Labarai ta Naija News ta fahimci cewa wannan sanarwan ya fito ne a kunshe a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aika wa Majalisar Dattawa a safiyar yau.

4. Bayani Daga Taron Sarakunan Gargajiya Na Arewa Da Ya Gudana A Kaduna

Manyan Sarakunan Gargajiya na Arewa sun gudanar da wata Babban Taronsu na 6 a jiya a Kaduna don tattaunawa kan abin da suka bayyana a matsayin kalubale da yawa da ke addabar yankin arewa, hadi da tarayyar kasar.

Shugaban kungiyar Sarakunan gargajiya na Arewa, Mai Martaba Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar, yayin da yake jawabi a wajen taron ya ce tabbatar da zaman lafiyar kasar itace babban fifiko a garesu.

5. ‘Yan Majalisa Suka Kafa Baki Ga Binciken Matakin DSS Kan Tsare Sowore

‘Yan Majalisan Najeriya sun hada kai da wasu manyan lauyoyi a kasar don yin Allah wadai da ayyukan hukumar ‘yan sanda sirrin (DSS), kan wani yunkuri na sake kame jagoran #RevolutionNow, Omoyele Sowore, a harabar babban kotun tarayya da ke Abuja.

Naija News ta samu labarin cewa gidan majalisar wakilan sun umarci wata kwamiti da su binciki lamarin da ya kai ga mamaye harabar kotun a ranar Juma’a.

6. ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji da ‘Yan Sanda A Wani Bidiyon da Suka Watsar A Yanar Gizo

Kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ta fitar da wani faifan bidiyo inda kungiyar ta Musulunci ta (Amaq) ta kashe wasu sojoji da wani dan sanda.

Wani sashin kungiyar ta’addar wadda ta yi rantsuwa da kungiyar ta Islamic State a yammacin Afirka ne ta fitar da bidiyon.

7. Fayose Ya Roki Mambobin Jam’iyyar PDP

Tsohon gwamna, Ayodele Fayose ya nemi mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ekiti da su yafe masa.

Ya yi wannan kiran rokon ne a lokacin da yake jawabi a gidansa da ke a Afao Ekiti, a wani taron zaman lafiya da ya yi da mambobin jam’iyya a kananan hukumomi 16 na Jihar.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa