Hukumar Tsaro sun kame wani mutum mai taimakawa Boko Haram a Maiduguri

Hukumar Tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) da ke a Jihar Borno, a ranar Laraba 5 ga watan Yuni ta sanar da kame wani mutumi mai suna Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 ga haifuwa da zargin samar da miyagun makamai da kayan hadin Bama-Bamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Maiduguri.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa bayanin Mista Ibrahim Abdullahi, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence ga manema labaran NAN, a Maiduguri, babban birnin Tarayyar Jihar Borno.

Mista Abdullahi ya bayyana da cewa rukunin tsaron su ta gane da Aliyu ne tun ranar 25 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, aka kuma kame shi a yayin da yake batun kai kayan hadin miyagun makamai ga ‘yan Boko Haram, kamar yadda ya saba yi.

Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Mata 29 da Yara 25 daga rukunin Boko Haram.

Bisa binciken hukumar NSCDC, sun gane da cewa Aliyu kan nemo wa ‘yan ta’addan Baturorin waya, Agogon hannu da kuma Kwamfuta (Laptop), wanda suke amfani da su wajen hadin bama-baman IEDs.

An kara da cewa lallai Aliyu ya dade da yin aikin, mutane sun sanshi ne da aikin tukin motar KEKE-NAPEP a cikin gari, amma yana da liki da ‘yan Boko Haram ba tare da sanin su ba.

Ha kazalika aka gane cewa yana da asusun ajiyar kudi da dama inda Boko Haram ke aika masa kudade don biyan sa ga aikin da yake masu.

Shugaban hukumar tsaron Civil Defence, Mista Mohammed ya bayyana cewa zasu bayar da Aliyu ga Rundunar Sojoi ta 7 Division Garison, don ci gaba da bincike akan dan ta’addan.

Karanta Sakon Shugaba Muhammadu Buhari ga Musulumai bayan Ramadan

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabi hukumar tafiyar da hidimar zabe ta Najeriya (INEC) don gudanar da aikin su da kyau duk da matsaloli da aka fuskanta a farko zaben.

News Naija Hausa ta gane da cewa shugaba Buhari ya gabatar da hakan ne a yayin da yake aika sakon Sallah ga ‘yan Najeriya ga bikin karshen azumin Ramadan.

A bayanin mataimakin Shugaban Kasa ga lamarin sadar da labaru, Malam Garba Shehu, ya sanar a birnin Abuja da cewa kafin a gudanar da zabe na shekarar 2019, annabawan hallaka ba su ba kasar damar samun zaman lafiya ba.

“Duk da wadannan tsoratar da mutane, kasar ta ci nasara da matsalolin siyasa” inji Shehu.

“Saboda watsi da harkokin kasuwancin su don kada kuri’a, masu jefa kuri’a sun nuna matukar kishin kasa a yayin da suka fita don yin aiki na gari.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce;

“Bari in sake amfani da wannan damar don sake tabbatarwa da dukan ‘yan Najeriya cewa sadaukarwanku na jefa mani kuri’a ba zai zama a banza ba. Zan tabbatar da cewa al’ummar kasar, musaman wadanda suka jefa kuri’u su ga tasirin gwamnati da shugabanci na” inji shugaban.

Da shugaban ya kafa baki ga zancen Ramadan, Shugaba Buhari ya bukaci Musulmi su sanya halin kwarai a gaba ba tare da son kansu ba.

“Lokacin hidimar Ramadan lokaci ne na karfafa a ruhaniya, sabili da haka, ya kamata mu yi amfani da addini a matsayin wahayi don aika halin da ya dace a kowane lokaci.”

“Dole ne a ci gaba da kyautata ga rayuwa harma bayan hidimar Ramadan. Komawa ga hanyoyi da halaye marasa kyau bayan Ramadan na iya rinjayar ainihin sako, koyaswa da kuma darussan da aka koya da karba a lokacin azumi” inji shi.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa cewa ‘yan Sandan Jihar Katsina sun Jefa wani Mutumi a Kurkuku da laifin kwanci da yaro na miji mai shekaru 10

Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da damar don nuna bakin ciki da kuma aika sakon ta’aziya ga wadanda ‘yan ta’adda suka hara, kashe ‘yan uwansu ko kuma yi masu barnan kayan zaman rayuka da sace-sace ‘yan uwansu a kasar.

Shugaba ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shugabancin sa ba zata bada dama ga ‘yan kisan gilla ba da rinjayar karfin shugabancin kasar.

“gwamnatin za ta bi su ba tare da jinkirta ba, za a kuma magance matsalar hare-hare a kasar a kankanin lokaci”

#EidAlFitr2019: Kalli Hotunan Shugaba Buhari a lokacin da ake Du’a’i a Masalacin Eid

Bayan da aka sanar a yau da tabbacin shiga watan shawwal da kuma tabbacin hidmar Sallar Eid Al Fitr ta shekarar 2019, Naija New Hausa ta gano da hoton shugaba Muhammadu Buhari tare da wasu manyan a kasar a lokacin da suke salla a masalacin Eid.

Naija News Hausa ta ci karo da hotunan ne bayan da Bashir Ahmad, mataimakin shugaba Buhari a lamarin sadarwa ta layin yanar gizo ya rabas da hotunan a shafin Twitter.

Kalli sakon da hotunan shugaba Muhammadu Buhari a kasa;

Shugaba Buhari yayi hidimar Sallar ne a Masalacin Eid da ke a Mabilla Barracks, anan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a yau 4 ga watan Yuni 2019.

KARANTA WANNAN KUMA; APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu kuma.

APC ta Jihar Zamfara sun kori Marafa da wasu mutane biyu kuma

Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu daga Jam’iyyar, akan laifin makirci ga Jam’iyyar.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar sun kori sanatan ne da ke wakilci a Zamfara Central a gidan Majalisa ta Takwas, hade da Hon Aminu Sani Jaji da kuma Mal Ibrahim Wakkala Liman.

An sanar da korar sanatan ne a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a birnin Abuja, ranar Litini da ta wuce, daga bakin Sakataren Sadarwa na yankin, Shehu Isah.

Matakin Jam’iyyar ga dakatar da Marafa ya kasance ne bisa ga zargin cewa ‘yan siyasan sun karya dokar Jam’iyyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawallen-Maradun ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr.

Bisa bayanin Mista Idris Yusuf Gusau, Daraktan Sadarwa ga Jihar ya bayyana cewa shanaye 750 da za a saya din za a rabar da su ne ga ragaggagu, gwamraye, yara marasa iyaye da ke a Jihar, don taimaka masu a wannan lokacin lokacin hidimar Sallah.

Gwamnan Zamfara ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr

Naija News Hausa ta karbi rahoto da tabbacin cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawallen-Maradun ya bada kudi naira Miliyan Tamanin da Takwas (N83,000,000) don sayan shanaye 750 ga hidimar Sallar Eid-El-Fitr a Arewacin kasar Najeriya.

Bisa bayanin Mista Idris Yusuf Gusau, Daraktan Sadarwa ga Jihar ya bayyana cewa shanaye 750 da za a saya din za a rabar da su ne ga ragaggagu, gwamraye, yara marasa iyaye da ke a Jihar, don taimaka masu a wannan lokacin lokacin hidimar Sallah.

Haka kuma Gwamnan, Matawallen-Maradun ya gargadi al’ummar jihar da yin amfani da wannan lokacin azumin Ramadan da kuma hidimar Sallar Eid-El-Fitr da ke gaba don neman fuskar Allah ga kwanciyar hankali, zamantakewa da ci gaba a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sanar da cewa jihar zata fara tsarafa manja a Zamfara.

“Za mu hada hannu tare da abokan kasashen waje don gabatar da itatuwan kwakwa don tsarafa manja a jihar” inji Matawallen-Maradun.

Ya kara da cewa jihar zata sake farfado da aikin noma don inganta shi hakan a Zamfara.

Kalli Jerin Suna da Lambar da Sarkin Musulumai yace a Kira idan an gana da Fitar Watan Shawwal

Mai Martaba Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni da ta gabata, ya yi kira ga Musuluman Najeriya duka da fita da maraicen ranar Litini don hangen sabon wata wanda zai bayyana karshen Azumun Ramadan ta shekarar 2019.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Sarkin Saudi Arabia ya gabatar da ranar Sallar Eid Al-Fitr

Sultan na Sokoto wanda shine kuma shugaban Kungiyar Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya taya dukan al’ummar Musulumai ta Najeriya da kuma dukan duniya murna ga hidimar Azumin Ramadan ta shekarar 2019. Shugaban a wata sanarwa da kungiyar NSCIA ta bayar, yayi Addu’a ta musanman da rokon Allah da amsa addu’a da Ibadar dukan musulumai a wannan Azumin Ramadan da ake batun karshe wa.

A cikin sanarwan; Sarki Sa’ad ya gargadi Musulumai duka da fita bayan faduwar ranar Litini, 3 ga watan Yuni 2019, don neman bayyanar Sabon Watan Shawwal 1440 AH, wanda ya bayyana cikar rana 29 ga Ramadani, 1440 AH.

Sanarwan ta kara da cewa idan har an gane da Fitar watan a ranar Litini, lallai mai Martaba Sarkin Musulumai zai gabatar da ranar Talata, 4 ga watan Mayu a matsayin rana ta farko ga watan Shawwal da kuma ranar Sallar Eid fitr.

Da cewa kuma, idan har ba a gan fitar watan ba a ranar Litini, Ramadan za ta ci gaba har zuwa ranar Talata, Ranar Laraba, 5 ga watan Yuni da ke biye zai tabbata ranar Farko ga Shawwal da kuma ranar Sallar Eid Fitr ta shekarar 2019.

Haka Kazalika aka bayar da jerin shugabannai da za a iya kira idan har an gane da Fitar Watan don Tabbaci. 

Kalli Sunayansu da Lambobin su a kasa;

  1. Sheikh Dahir Bauchi                           – 08036121311 – [email protected]
  2. Sheikh Karibullah Kabara                   – 08035537382 – [email protected]
  3. Mallam Simwal Usman Jibrin             – 08033140010 – [email protected]
  4. Sheikh Salihu Yaaqub                        – 07032558231 – [email protected]
  5. Mallam Jafar Abubakar                      – 08020878075 – [email protected]
  6. Alhaji Abdullahi Umar                        – 08037020607 – [email protected]
  7. Professor J.M. Kaura                           – 08067050641 – [email protected]
  8. Dr. Bashir Aliyu Umar                         – 08036509363 – [email protected]
  9. Sheikh Habeebullah Adam Al-Ilory    – 08029032575 – [email protected]
  10. Ustaz Nurudeen Ibrahim                   – 08027091623 – [email protected]
  11. Muhammad Rabiu Salahudeen         – 08035740333  – [email protected]
  12. Sheikh Abdur-Razzaq Ishola              – 08023864448, 08051111063 – [email protected]                                  sheikh@[email protected]
  13. Sheikh Abdur Rasheed Mayaleke       – 08035050804 – [email protected]
  14. Dr. Ganiy I. Agbaje                              – 08028327463, 08057752980 – [email protected] [email protected]
  15. Gafar M. Kuforiji                                  – 08033545208 – [email protected]
  16. Professor Usman El-Nafaty                 – 08062870892 – [email protected]
  17. Mallam Ibrahim Zubairu Salisu           – 08038522693 – [email protected]
  18. Dr. Usman Hayatu Dukku                    – 0805 7041968 – [email protected]
  19. Imam Manu Muhammad                    – 08036999841 – [email protected]
  20. Qadee Ahamad Bobboy                      – 08035914285 – [email protected]
  21. Professor Z. I. Oboh Oseni                   – 08033574431 – [email protected], [email protected]
  22. Nurudeen Asunogie D.                        – 08033533012 – [email protected]
  23. Sheikh Bala Lau                                    – 08037008805, 08052426880 – [email protected]
  24. Sheikh Sani Yahaya Jingir                     – 08065687545 – [email protected]
  25. Sheikh AbdurRahman Ahmad              – 08023141752 – [email protected]
  26. Muhammad Yaseen Qamarud-Deen   – 08055322087 – [email protected]
  27. Sheikh Lukman Abdallah                      – 08052242252 – [email protected]
  28. Sheikh Sulaiman Gumi                         – 08033139153 – [email protected]
  29. Sheikh Adam Idoko                              – 08036759892 – [email protected]
  30. Alhaji Yusuf Nwoha                              – 08030966956, 08026032997 – [email protected]

Sabon Gwamnan Jihar Yobe, Buni ya Auri diyar tsohon Gwamnan Jihar rana ta biyu da rantsar da shi

Gwamnan Jihar Yobe ya kara Mata guda bisa biyu da yake da su a da

Naija News Hausa ta  karbi rahoto da cewa sabon gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da aka rantsar ga kujerar Gwamna a ranar Alhamis, 29 ga Mayu 2019 da ta gabata ya kara Aure rana ta biyu ga rantsar da shi.

Bisa fahimtar gidan labaran nan tamu, yarinyar mai suna Ummi Adama Gaidam, diya ce ga tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam.

A halin yanzu, bincike ta nuna da cewa yarinyar na kasar Saudi Arabia tana karatu, idan kuma ta kamala sai ta dawo da zama matar Gwamnan ta Uku.

Bisa bayanin wani da ke da cikakken sani ga lamarin, ya bayyana da cewa lallai Mista Buni ne ya nemi Ummi da Aure ba tare da sanin tsohonta ba, ko da shike wai yayi hakan ne don karfafa dankon siyasar shi da babban ta Gaidam.

Rahotannai sun bayar da cewa anyi auren ne a nan cikin gidan Malam Gaidam da ke a Sabon Fegi, Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

“An dauki duk matakai da ya kamata ga aure, harma da bayar da kwamdunan Goro dadai sauran su, aka kuma aurar da Fatima a gaban kanancin ‘yan uwan su” inji mai bada bayani, ko da shike yayi rokon cewa kada a gabatar da sunan sa”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya aika sakon Soyayya ga Matarsa Dolapo da nuna mata godiya, musanman yadda ta bashi hadin kai da nuna mashi so a shugabancin su ta farko.

Saudi Arabia ta gabatar da ranar Sallar Eid al-Fitr

Hadaddiyar Kasar Saudi ta gabatar da Kwamitin da zasu fita hangen Wata don Sallar Eid

Ministan Shari’ar kasar Saudi Arabia, Sultan bin Saeed Al Badi Al Dhaheri, ya bayyana cewa kwamitin zasu hade a jagorancin sa hade da wasu Manyan Ofisoshi bayan sallar Maghrib ranar Litini, 3 ga watan Yuni, watau rana ta 29 ga watan Ramadani.

Bisa bayaninsa, zasu yi zaman ganawar ne a ranar Litini ta gaba a nan gidan shari’a da ke a birnin Abu Dhabi.

Ministan ya kuma shawarci Alkalan Kotun Shari’a da ke a kasashe da fita neman bayyanar sabon watar, su kuma sanarwa kwamitin inda an gane da watar a ko ta ina.

“Idan ba a gan watar ba a maraicen ranar Litini, Tabas za a ci gaba da azumin Ramadani a ranar Talata. Amma idan har an gane da fitar watar a ranar Litini, lallai ranar Talata, 4 ga watan Yuni ya tabbata, Shawwal 1, watau ranar Sallar Eid Fitr” inji Saeed.

KARANTA WANNAN KUMA; Ka Manta da zancen Gina wa Fulani Gidan Radiyo, Urhobo sun Kalubanlanci Buhari

Hukumar EFCC sun kame Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Okorocha da Matarsa

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma Kare Tattalin Arzikin Najeriya (EFCC) ta kame Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, hade da matarsa Nkechi Okorocha.

Bisa bayanarwar rahotonnai, Hukumar sun kame shi ne da kuma wasu ‘yan uwan sa da ke zama da shi, Gerald Okorocha, Okey Okorocha, aka kuma katange babban makarantar Jami’a ta Eastern Palm University da yake da ita a Ogboko, Jihar Imo.

Ko da shike a lokacin da aka bayar da wannan rahoton, Naija News Hausa ba ta samu gane da wata bayani ba game da kame Okorocha daga bakin shugaban Hukumar EFCC ko wani ma’aikaci da Ofishin su.

Zamu sanar a layin Hausa.NaijaNews.Com idan mun samu tabbaci ko karin bayani da rahoton.

An gane da Gawar wata Yarinya a cikin Rijiya a Jihar Kano

Hukumar Yaki da Gobarar Wuta ta Jihar Kano, ta sanar da cewa ranar Talata da ta gabata sun gane da gawar wata ‘yar karamar yarinya mai shekaru 11 a ciki rijiya.

An gano gangan jikin yarinyar ne da aka bayyana sunan ta da Fatima Abdullahi a cikin wata Rijiya a shiyar Zaura Ganduje, a karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

Kakakin yada yawun, Alhaji Saidu Mohammed, ya bayyana ga Kungiyar Manema Labaran Najeriya (NAN) a Jihar Kano cewa sun gane da hakan ne a safiyar ranar Talata da ta wuce.

A bayanin Mohammed da manema labaran NAN, ya bayyana cewa hukumar su ta karbi kirar gaugawa ne daga  Dawanawu cewa wata karamar yarinya ta fada a cikin rijiya.

Ya kara da cewa lallai kamin isar ma’aikata a wajen, yarinyar ta riga ta mutu.

Ya kuma bayyana cewa bayan da hukumar ta gane da gawar yarinyar, sun dauke ta da mika ta ga wakilin garin Zaura, Alhaji Idris Shua’ibu.

“Har yanzu ana kan bincike ga sanadiyar da ya kai yarinyar a cikin rijiyar” inji shi.