Connect with us

Uncategorized

Hukumar Tsaro sun kame wani mutum mai taimakawa Boko Haram a Maiduguri

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) da ke a Jihar Borno, a ranar Laraba 5 ga watan Yuni ta sanar da kame wani mutumi mai suna Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 ga haifuwa da zargin samar da miyagun makamai da kayan hadin Bama-Bamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Maiduguri.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa bayanin Mista Ibrahim Abdullahi, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence ga manema labaran NAN, a Maiduguri, babban birnin Tarayyar Jihar Borno.

Mista Abdullahi ya bayyana da cewa rukunin tsaron su ta gane da Aliyu ne tun ranar 25 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, aka kuma kame shi a yayin da yake batun kai kayan hadin miyagun makamai ga ‘yan Boko Haram, kamar yadda ya saba yi.

Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Mata 29 da Yara 25 daga rukunin Boko Haram.

Bisa binciken hukumar NSCDC, sun gane da cewa Aliyu kan nemo wa ‘yan ta’addan Baturorin waya, Agogon hannu da kuma Kwamfuta (Laptop), wanda suke amfani da su wajen hadin bama-baman IEDs.

An kara da cewa lallai Aliyu ya dade da yin aikin, mutane sun sanshi ne da aikin tukin motar KEKE-NAPEP a cikin gari, amma yana da liki da ‘yan Boko Haram ba tare da sanin su ba.

Ha kazalika aka gane cewa yana da asusun ajiyar kudi da dama inda Boko Haram ke aika masa kudade don biyan sa ga aikin da yake masu.

Shugaban hukumar tsaron Civil Defence, Mista Mohammed ya bayyana cewa zasu bayar da Aliyu ga Rundunar Sojoi ta 7 Division Garison, don ci gaba da bincike akan dan ta’addan.