Connect with us

Uncategorized

Sabon Hari a kauyen Zamfara: Mutane 22 sun rasa rayukan su

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu masu makaman linzami sun kai hari a garin Malikawa, wani kauye a Gidan Goga a Zamfara. Wannan shi ne hari na biyu a tsakanin yan watanni da nan.

Wannan hari ya tafi da rayukan mutane ashirin da biyu 22 ko, da kuma mutane da dama da suka sami raunuka.

Wani mazaunin wannan kauye ya tabbatas mana da wannan.

Yan Jaridun Daily Trust sun bada rihoton cewa wasu Yan Hari da bindiga da ba a san su ba sun shigo wannan gari ne da Babura da dama, sun fado masu da hari da halbin mutane kawai ba dalili.

“Na dawo ne daga gona da maraice karfe Hudu 4:00 na shiga wanka ke nan na ji kuwa da ihu na mutane, suna kira ga taimako. Na fito daga wanka ke nan na taras da jama’an gari cikin mawuyacin hali ana kuka da ihu cikin azabar wannan hari.

“Kowa da kowa na ta gudu, da yara da manya duka neman taimako. Na gane da cewa muna cikin mugun hali da wadannan yan hari da suka shigo da babura da harbin mutane ko ta ina.

“Ko kafin in ce na nemi hanyar tsira, yan harin nan sun cin ma kofar gida na. yarda na tsira abin mammaki ne gare ni har yanzu, ”Wani daga cikin mazaunin kauyen ya fada da cewa an kone mutane shidda da ransu.

Wani mazaunin wannan kauyen ya fada da cewa a lokacin da aka bi mutane shidan nan, sun ratsa cikin wani tarin masara amma ba su san da cewa yan harin nan su hango su ba. suna isa garesu suka haska masu wuta duka har suka kone.

“A yadda nike maka bayyani yanzun nan, ina cikin kauyen Boko neman kananan yaran da suka bacce tun bayan harin nan jiya bamu sa su a ido ba. wadanda kuma suka mutu an bizne su duka.

Rihoto ta bayyas da cewa ba a samu kalma da Shugaban Yan Sanda na wannan wurin ba, watau mai suna SP Muhammad Shehua a lokacin da wannan mugun abin ya faru.