Connect with us

Labaran Najeriya

‘Dalilin da ya sa Mutumin da ke Aso Rock ba Buhari bane da muka zaba’ – Bolaji Abdullahi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sakataran Yada Labarai na Kungiyar APC na da Bolaji Abdullahi ya bada bayani akan dalilin da ya sa ba Muhammadu Buhari da Najeriya ta zaba a Shekara ta 2015 ke cikin Aso Rock ba.

Abdullahi, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka juya daga PDP zuwa APC ya ce wa yan Najeriya su sauka daga jirgin yaudara ta Buhari. da cewa mutumin da muka zaba a shekara ta 2015 ba shi ne ke kan mulki ba.

Ya fadi wannan ne yan Jarida ta Vanguard.

Yace da yawa cikin mu sun fada cikin yaudarar siyasa har sun bada kansu wajen yiwa Muhammadu Buhari kampen a shekara ta 2015. yanzu kuma mun gane da cewa karya ne ke ciki duka da yaudara.

“Manyan Shugabanan Arewa sun kasance daya daga cikin masu karfi da suka bawa Buhari goyon baya a shekara ta 2015, amma yanzu kuma duk sun gane da cewa ba Shugaban da muka zaba a shekara ta 2015 ke a sama ba yanzu.

“Yanzun ma Buhari ya jawo yan cin hanci da rashawa duka ya sa a kungiyar sa da mulkin sa”.