Connect with us

Labaran Najeriya

Albashi: Naira Dubu 30,000 bai isa ga Ma’aikatan Kasa ba – inji Dogara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kakakin yada yawu na Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya gabatar a yau Litini a birnin Abuja da cewa Naira dubu 30,000 na sabon tsarin Kankanin Albashin Ma’aikata da Kungiyar Ma’aikatan kasa ke bukatar gwamnati da ya kasa ma ga ma’aikata.

Yace, “Idan har ana bukatar a magance Cin hanci da Rashawa a kasar nan, dole ne a biya kudi isashe ga ma’aikata, bama kawai naira dubu talatin ba na kankanin albashi” in ji Dogara

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Gwamnatin Tarayya ta yarda da naira dubu 27,000 a matsayin sabon kankanin albashin ma’aikata.

Wannan shine sakamakon tattaunawar da aka yi a ranar Talata, 22 ga watan Janairu, 2019 da ta halarci Manyan shugabannai kamar tsohon shugaba Goodluck Jonatha, Abdulsalami Abubakar, Olusegun Obasanjo, Sanata Bukola Saraki tare da wasu Gwamnonin Jihohin kasar a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo.

Ko da shike bayan matakin da Majalisar Dokoki ta Jiha da shugabancin kasa ta yi a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, na amincewa da biyar kankanin albashi na naira dubu 27,000 kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa.

‘Yan Kungiyar Mallaman Tarayya ta Kasar Najeriya (NUT) da Hukumar Kungiyar Ma’aikatan kasa (NLC) bayyana rashin amincewarsu game da batun biyar 27,000. sun ce dole ne gwamnatin tarayya ta karasa 3,000 ga 27,000 don kai ga arjejeniyar su.

Yakubu Dogara ya ce, “Naira Dubu 30,000 bai isa ga Ma’aikatan Kasa ba ganin irin tsadar abubuwa a kasar”

“Idan kuma ana son lallai a magance cin hanci da rashawa a kasar, dole ne a biya ma’aikata kudi isashe” in ji shi.

Ya fadi wannan ne a gabatarwa da yayi ga Ma’aikatan gudanar da Zaben kasa game da kankanin albashin.

 

Karanta kuma: Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga dokar dama ga Kamfanoni wajen tsarrafa hanyoyi a kasar