Connect with us

Uncategorized

Yan Sanda: IGP Mohammed Adamu ya Sanya sabbin DIGs

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu a yau Litini 28 ga Watan Janairu ya sanya sabbin DIGs guda shidda.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa IGP Mohammed ya tsige wasu DIGs guda shidda daga matsayin su da safen nan.

Sanarwan da muka bayar daga Manyan Jaridun Najeriya ta ranar yau Litini na kamar haka;

Sabon shugaban Jami’an tsaron ‘yan sanda Najeriya, IGP Muhammed Adamu ya dakatar da dukan mataimakan Inspekta da ke karkashin sa. Ko da shike wadannan DIGs da ya dakatar sun dade ga aikin tsaron kasar kamin zuwar Adamu, kuma sun yi aiki tare da shugaban jami’an tsaron na da, Ibrahim Idris.

IGP Adamu ya gabatar da wannan nadin ne bayan ‘yan awowi kadan da ya dakatar da DIGs da ke karkashin sa duka don gudanar da  irin nasa tsarin ta hanyar doka.

Ga sunayen sabbin DIGs da aka daukaka daga matsayin Mataimakin Insfekta Jenar zuwa Matsayin DIG da takaitace labarin aikin su:

  • Usman Tilli Abubakar – ya shiga aikin tsaron ne a watan Fabrairu a shekara ta 1976 daga Jihar Kebbi
  • Abdulmaji Ali ya shiga aikin tsaron ne a watan Fabrairu a shekara ta 1986 daga Jihar Neja
  • Taiwo Frederick Lakanu ya shiga aikin tsaron ne a watan Fabrairu a shekara ta 1986 daga Jihar Legas
  • Godwin Nwobodo ya shiga aikin tsaron ne a shekara ta 1984 daga Jihar Enugu

Sauran DIGs biyun kuma an daukaka su ne daga matsayin Kwamishanan zuwa matsayin DIGs

Sunayen su na kamar haka:

  • Ogbizi Michael – Tsohon Kwamishanan ‘Yan Sandan Jihar Abia
  • Michael Lamorde – Ciyaman na Kulawa da karar Tattalin Arzikin da Tasirin Kasa na da, daga Jihar Adamawa.

 

Karanta Kuma: Cutar Lassa Fever ya dauke rayuka 5 a Jihar Plateau.