APC: Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Imo da Abia a yau

A yayin da zaben tarayya ke gabatowa, Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihohin kasar guda biyu a yau don yakin neman sake zabe.

Ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa Jihohin zai kasance ne a yau Talata 29 ga Watan Janaiaru, 2019, a yayin da shugaban zai sauka a filin jirgin saman Sam Mbakwe da ke birnin Owerri kamin ya kama hanya zuwa fillin wasan kwallon kafa in da za a gudanar da hidimar.

An umurci mambobin Jam’iyyar APC duka da ke Jihar da su tabbatar da cewa hidimar an gama shi ne cikin lafiya ba tare da wata tashin hankali ba ko hitina, da kuma cewa su yi kokarin halartar hidimar, a yayin da shugaban kasa zai yi gabatarwa ga ‘yan Jam’iyyar duka.

Rochas Okorocha, Gwamnan Jihar Imo ya bukaci jama’ar Jihar da su kasance da addu’a da rokon Allah ya saukar da shugaba Muhammadu Buhari lafiya zuwa wajen hidimar.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa dan takaran Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Imo makon da ta gabata don kadamar da yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a Jihar.

Ya kuma bukaci jama’ar Jihar da su tabbatas da cewa an gudanar da hidimar yadda ya kamata, kuma da tabbatar da cewa hidimar ya kasance hidima mafi daraja bisa dukan hidimar yakin neman zaben da aka saba yi da baya.

Haka kuma shugaban zai halarci filin kwallon Dan Anyiam da ke Jihar Abia bayan barin Imo, a yayin da Dokta Orji Uzor Kalu, Gwamnan Jihar zai marabce shi.

 

Karanta kuma: Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga dokar dama ga Kamfanoni wajen tsarrafa hanyoyi a kasar Najeriya