Uncategorized
Ba wanda ya ji mugun rauni a faduwar Dakali na Jihar Kebbi – PDP
Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, Mallam Ibrahim Omie ya bayyana da cewa babu wanda yaji wata mugun rauni sakamakon dakali da ya fadi da ‘yan siyasa wajen hidimar rali da Jam’iyyar ta gudanar a kwanakin baya.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wata bidiyo da ke nine da ‘yan Jam’iyyar PDP da suka fadi sanadiyar tsinkewar dakali a Jihar Kebbi ta mamaye yanar gizo, kamar yadda muka sanar.
Abin ya faru ne a wajen ralin yakin neman zabe na dan takaran Gwamnan Jihar Kebbi na Jam’iyyar PDP, Alhaji Abubakar Malam.
#PDP STAGE COLLAPSE! pic.twitter.com/iiTBIBeUNJ
— Salisu Nurudeen (@SalisuNurudeen1) January 29, 2019
“Wadanda abin ya faru da su, sun sami kulawa a asibiti, ko da shike basu ji wata muguwar rauni ba” inji Omie.
Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa, bidiyon ya rigaya ya mamaye kota ina a yanar gizo.
Ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar, Mallam Haruna B. Saidu ya ce bayyana da cewa ‘yan adawa ne suka aikata wannan hali na yadar da bidiyon.