Connect with us

Uncategorized

Ba wanda ya ji mugun rauni a faduwar Dakali na Jihar Kebbi – PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, Mallam Ibrahim Omie ya bayyana da cewa babu wanda yaji wata mugun rauni sakamakon dakali da ya fadi da ‘yan siyasa wajen hidimar rali da Jam’iyyar ta gudanar a kwanakin baya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wata bidiyo da ke nine da ‘yan Jam’iyyar PDP da suka fadi sanadiyar tsinkewar dakali a Jihar Kebbi ta mamaye yanar gizo, kamar yadda muka sanar.

Abin ya faru ne a wajen ralin yakin neman zabe na dan takaran Gwamnan Jihar Kebbi na Jam’iyyar PDP, Alhaji Abubakar Malam.

“Wadanda abin ya faru da su, sun sami kulawa a asibiti, ko da shike basu ji wata muguwar rauni ba” inji Omie.

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa, bidiyon ya rigaya ya mamaye kota ina a yanar gizo.

Ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar, Mallam Haruna B. Saidu ya ce bayyana da cewa ‘yan adawa ne suka aikata wannan hali na yadar da bidiyon.

Karanta kuma: Wata kyakyawar yarinya ta tsarafa wata bidiyo inda ta kafa baki da waka na yabon Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.