Connect with us

Uncategorized

Kimanin mutane 60 suka mutu a harin da aka yi wa Gwamnan Kano, Kashim Shettima

Published

on

at

A ranar Jumma’a da ta gabata, ‘yan awowi kadan da soma zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai, ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi wa Gwamnat Kashim Shettima da mabiya bayan sa hari a Jihar Borno, inda suka kashe kimamin rayuka 60 kamar yadda muka sami rahoto hakan.

Mun samu tabbacin rahoton ne ‘yan lokatai kadan da ta wuce da cewa Boko Haram sun tari gwamna Shettima ne da mabiyansa a yayin da suke kan hanyar zuwa Gamboru Ngala, wata kauyan Jihar da ke kusa da bodar kasan Kamarun.

A cikin bayanin gwamnan, yace “Mutane ukku suka mutu a gaba na, wani soja guda da manyan mutane biyu da ke tare da ni” inji shi.

Da aka binciki wani da ya samu tsira daga harin, ya ce “akilla, na hangi gawar mutane kusan 40. haka kuwa wata rukuni itama ta bayar da cewa watakila gawarwaki da suka gani ya kai 100.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa farmaki ya tashi a jihar Kano, inda aka tare Rabiu Kwankwaso da mabiyansa har an kashe mutane biyu da kone motoci da dama kurmus da wuta.

Mun iya ganewa a Naija News da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun samu gujewa da kimanin mutane 100 zuwa 200 a wajen wannan harin. Mun kuma samu rahoto da cewa an kai gawarwaki kusan 60 zuwa wata asibitin da ke a garin Maiduguri.

“Sun fado mana ne da motocin akorikura guda biyu daga gaban mu, ko kamin mu yunkura, sai ga wasu kuma daga gefen mu sanye da kayakin sojoji” inji fadin wani jami’in tsaro da ya samu tsira daga harin.

“Kusan mutane 200 suka yi gudun hijira don tsira daga mumunar harin”

Karanta wannan kuma: Allah ne kawai ke iya dakatar da zaben ranar Asabar – inji Farfesa Mahmood