Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 2 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 2 ga Watan Satunba, 2019

1. An Kashe Sojojin Najeriya 3 da yiwa 8 A Cikin su Raunuka a Rikici da Boko Haram

Sojoji Uku na Sojojin Najeriya sun rasa rayukansu yayin da wasu 8 suka sami raunuka bayan wata musayar wuta da ‘yan kungiyar Boko Haram a kan hanyar Monguno-Mairari-Gajiram.

Naija News ta fahimci cewa munsayar wutan ya auku ne a ranar Juma’a 30 ga watan Agusta tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da rukunin sojojin na sashi na 3 ta Operation Lafiya Dole wanda ke tsaron Super Camp Monguno.

2. An fara kafa Ruga a Jihar Zamfara

A ranar Talata da ta gabata ne aka tsara shirin Ruga a jihar Zamfara bayan gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ba umarnin da sanarwar fara ayyukan kafa Ruga ga makiyaya a cikin jihar.

Naija News ta fahimci cewa Gwamnan jihar ya ba da wannan umarnin ne a ranar Asabar bayan karbar sabon shirin Ruga daga hannun mai ba da shawara kan ayyukan, Mista Emmanuel Ozigi.

3. A Karshe CAN ta mayar da Martani game da hidimar RUGA

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi watsi da shirin RUGA da aka shirya.

Naija News ta ba da rahoton cewa Fasto Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya baiyana matsayin kungiyar a yayin taron shugabannin Ikilisiyoyi a birnin Legas a ranar Asabar, 31 ga Agusta da ta wuce.

4. Shugaba Buhari Ya dawo kasar Najeriya daga kasar Japan

Shugaba kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Asabar din da ta gabata ya sauka Najeriya a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Naija News ta ba da rahoton cewa isowar shugaba Buhari ya biyo ne bayan kamala Babban Taron Kasa da Kasa na Bakwai kan Ci gaban Afirka (TICAD 7) da ya halartar a Yokohama, kasar Japan.

5. Buratai Ya Ziyarci Dakarun Sojojin Najeriya Bayan Hari

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai ya kai ziyarar bazata ga rundunar Sojojin Najeriya a fagen daga ta Operation Lafiya Dole a Borno.

Naija News ta fahimci cewa ziyarar Burutai ya biyo bayan wani mumunar harin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi ga sojojin a kauyen Gasarwa, kan hanyar Gajiram-Monguno da ke cikin Karamar Hukumar Nganzai na Borno a ranar Asabar.

6. Fasto Adeboye Ya mayar da Martani game da hidimar RUGA

Babban Fasto da Janar na Ikilisiyar ‘The Redeemed Christian Church of God (RCCG)’, Fasto Enoch Adeboye, ya ce ya goyi bayan adawar kungiyar Christian Association of Nigeria (CAN) game da zance a dakatar da hidimar kafa RUGA.

Naija News Hausa ta tuna da cewa kungiyar a baya ta kira ga Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi watsi da shirin RUGA da aka shirya.

7. Shugaban ‘Yan Sanda ya bada umarnin a kama Shugabannin ‘Yan Shi’a A Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ba da umarnin kame dukkan shugabannin kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) a dukkanin jihohin kasar 36.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne bayan da shugaban Jami’an tsaron, Sufeto-janar (IGP), Mohammed Adamu ya ba da umarnin a karshen mako da ta wuce.

8. Abinda Magashi ya fada wa Sojoji a Maiduguri

Ministan Tsaro, Maj.-Gen. Bashir Magashi (Rtd), ya yi alkawarin tsanantawa gwamnatin tarayya don inganta tsarin kulawa ta musanman ga rundunar sojojin Najeriya.

Naija News ta fahimci cewa Magashi (Rtd) ya ce manufar kyautata ga kulawa ga sojojin Najeriyar mataki ne da zai karfafa su da kuma kara masu inganci da karfi wajen yaki da ta’addanci a kasar.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

‘Yan Kunar bakin wake sun kashe mutane fiye da ashirin a wata tashin Bam a Borno

Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da cewa fiye da mutane 20 wasu ‘yan kunar bakin wake suka kashe da tashin bam a wata gidan kallon wasa da ke a Konduga, nan Jihar Borno.

Bisa rahoton da aka bayar ga Naija News Hausa, An sanar da cewa kimanin mutane 30 suka samu raunuka daban-daban a harin.

Mumunar lamarin ya faru ne bayan da wasu mutane biyu, mace da namiji da ake zargi da zaman ‘yan ta’addan Boko Haram, da ke dauke da kayan bam na (IED) suka hari wani gidan kallon wasa da ke gaba ga wata Asibitin Mandarari, a karamar hukumar Konduga, missalin karfe Tara na daren ranar Lahadi da ta gabata.

Ko da shike an samu cin karo da wata ‘yar mace kuma da ke dauke da kayan bam na IED, da aka gane da ita sai aka kame ta tun bata fashe da bam din ba, aka kuma mikar da ita ga rundunar tsaron sojojin.

Ka tuna da cewa mun sanar a Naija News Hausa a baya cewa ‘Yan Hari da Bindiga sun sace Wakilin Garin Labo a Jihar Katsina

Hukumar Tsaro sun kame wani mutum mai taimakawa Boko Haram a Maiduguri

Hukumar Tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) da ke a Jihar Borno, a ranar Laraba 5 ga watan Yuni ta sanar da kame wani mutumi mai suna Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 ga haifuwa da zargin samar da miyagun makamai da kayan hadin Bama-Bamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Maiduguri.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa bayanin Mista Ibrahim Abdullahi, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence ga manema labaran NAN, a Maiduguri, babban birnin Tarayyar Jihar Borno.

Mista Abdullahi ya bayyana da cewa rukunin tsaron su ta gane da Aliyu ne tun ranar 25 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, aka kuma kame shi a yayin da yake batun kai kayan hadin miyagun makamai ga ‘yan Boko Haram, kamar yadda ya saba yi.

Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Mata 29 da Yara 25 daga rukunin Boko Haram.

Bisa binciken hukumar NSCDC, sun gane da cewa Aliyu kan nemo wa ‘yan ta’addan Baturorin waya, Agogon hannu da kuma Kwamfuta (Laptop), wanda suke amfani da su wajen hadin bama-baman IEDs.

An kara da cewa lallai Aliyu ya dade da yin aikin, mutane sun sanshi ne da aikin tukin motar KEKE-NAPEP a cikin gari, amma yana da liki da ‘yan Boko Haram ba tare da sanin su ba.

Ha kazalika aka gane cewa yana da asusun ajiyar kudi da dama inda Boko Haram ke aika masa kudade don biyan sa ga aikin da yake masu.

Shugaban hukumar tsaron Civil Defence, Mista Mohammed ya bayyana cewa zasu bayar da Aliyu ga Rundunar Sojoi ta 7 Division Garison, don ci gaba da bincike akan dan ta’addan.

Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Mata 29 da Yara 25 daga rukunin Boko Haram

Rukunin Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation LAFIYA DOLE sun gabatar da ribato mata 29 hade da ‘yan yara 25 a wata kangin ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Jihar Borno.

Bisa ganewar Naija News Hausa, Rundunar Sojojin sun samu nasarar hakan ne a wata yawon hadin kai da suka yi na ‘yan bangan Jihar Borno a ranar 11 ga watan Mayu da ta wuce, inda suka fada wa kauyan Ma’allasuwa da Yaga – Munye ta Jihar Borno da binciken ‘yan ta’adda.

Ko da shike ‘yan ta’addan Boko Haram din basu jira isar rundunar Sojojin ba, sai suka hari daji da gudu, suka kumar bar tarin mutane 54 da ake zaton cewa an sace su ne daga filin hari.

A cikin mutane 54 da ‘yan ta’addan suka bari, an taras da samun tarin Mata 29 da kuma kananan yara, maza da mata 25.

A cikin yawon zagayen Rundunar Sojojin, an bayyana da cewa sun taras da Motocin Yakin ‘yan Boko Haram biyu a Zari – Kasake da kuma kauyan Jumachere a karamar hukumar Mobbar ta Jihar Borno, sun kuma rushe su da kayakin da ke a cikin su.

A garin hakan ne kuma suma taras da wani da ake diba da jami’a in tsaron ‘yan sanda masu yawo (Mopol), Sergeant Markus John, mai lamba kaki- PNo 383106.

Rundunar Dakarun Tsaron sun bayar da cewa sun ci karo ne da shi a rukunin tsaron su da ke a Njimtilo ta shiyar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. An gane shi ne da Miyagun Makamai kamar (magazines 2), da kuma wasu kayakin yaki da dama cikin jakkar da yake tafiya da ita zuwa Jihar Legas.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Sojojin Najeriya sun kame masu Kira da Samar da Makami ga ‘yan Ta’adda a Kontagora (Neja) da Katsina

Boko Haram: An Kashe mutane 7 da Sojoji 3 a garin Molai ta Jihar Borno

Boko Haram sun kai sabuwar hari a Jihar Borno da dauke rayukan mutane kimanin 10

Naija News Hausa ta karbi rahoto cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun hari yankin Molai da ke mafitar garin Maiduguri, da maraicen ranar Talata da ta wuce, inda suka kashe kimanin rayuka goma.

Wannan abin ya faru ne a garin Molai da ke a karamar hukumar Jere ta Jihar Borno. 

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wasu ‘Yan hari da Makami sun kashe wani Sarki a kauyan Balle da ke yankin Jihar Sokoto, inda suka kone Ofishin Jami’an tsaro da motocin su biyu a ranar Talata da ta wuce.

A wannan hari da aka kai a garin Molai, an sanar da cewa fiye da mutane 100 ne aka bari huntu da rashin gidaje a yayin da ‘yan ta’addan suka kone masu gidajen kwanan su.

Ba gidaje kawai ba, mazaunan wajen sun bayyana da cewa ‘yan ta’addan sun kone rukunonin tsaron rundunar Sojoji da ke a shiyar.

Mallam Isa Kagama, wani mazaunin kauyan Balle ya bayyana ga manema labarai cewa sun rasa rayukan mutanen su bakwai (7) a harin.

“Kimanin mutane Goma (10) ne ‘yan ta’addan suka kashe, Sojoji Ukku da kuma mutane 3 daga kauyan Maiboriti, mutum 4 kuma daga kauyan Molai.”

“A halin yanzu ‘yan ta’addan sun barmu da rashin gidajen barci, kayakin mu duk sun kone, harma sun lallace Injimi Wutan Lantarki da ke samar da wutan lantarki ga dukan garin Maiduguri; ku dube mu, duk mun lallace.” inji Malam Isah.

Ko da shike manema labarai, a lokacin da aka karbi wannan rahoton ba a samu karban bayani daga wata hukumar tsaro ba, amma watakila hakan zai faru idan an jima.

KARANTA WANNAN KUMA; Mutuwa rigan Kowa! Maman Sanata Dino Melaye ta riga mu zuwa Gidan Gaskiya

Boko Haram sun kashe Sojoji 5, Talatin kuma sun bata a Jihar Borno

Kimanin Sojojin Najeriya biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar ganawar wuta da ‘yan Boko Haram a Jihar Borno.

Naija News Hausa ta karbi rahoto a yau Litini da cewa Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun yi wata ganawar wuta da ‘yan ta’adda a ranar Jumma’a da ta gabata, inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka samu cin nasara da kashe sojoji biyar daga cikin sojojin Najeriya a nan take.

Bisa bayanin wani da bai bayar da sunan sa ba ga manema labarai, ya gabatar da cewa Rundunar Sojojin kasar sun samu gano da gawakin sojoji biyar da aka kashe. “An gano gawakin Sojoji biyar da suka mutu amma har yanzu ba a samu ganin kimanin sojoji Talatin ba da suka halarci ganawar wutan”

Ya kara da cewa har wa yau Rundunar sojojin na cikin bincike da neman sojoji kimanin 30 da suka bata a harin wanda ba wanda ya san inda suke, inji shi.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa ‘yan ta’addan da aka fi sanin sunar kungiyan su da ‘ISWAP’ ne suka hari rukunin Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya a ranar Jumma’a da ta wuce a rukunin su da ke a shiyar Mararrabar Kimba, mai Kilomita 135 daga garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Mun ruwaito a baya a shafin Labaran Hausa ta gidan yada labaran mu, da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Dokar ƙuntatawa na tsawon awowi 24 a Jihar.

An gabatar ne da dokar ƙuntatawa a ranar 26 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 a layin yanar gizon nishadarwa ta Facebook, kamar yadda Samuel Aruwan, Kakakin yada yawun Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya rabar.

Kalli Bidiyon Saukar Shugaba Muhammadu Buhari yau a Maiduguri

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a yau Alhamis.

Naija News na da sanin cewa Shugaban ya ziyarci Jihar ne don kadamar da wasu ayuka da aka yi a Jihar ta fanin; Ilimi, Kiwon Lafiyar Jiki, Samar da Hanyoyi dadai sauran su.

Wannan ziyarar Buhari ya biyo ne bayan dawowar shi daga Jihar Legas a wata ziyara da shugaban ya je don kadamar da wasu sabbin ayuka da aka yi a Jihar.

Kalli saukar Mai Girma, Shugaba Muhammadu Buhari daga Jirgin Sama a Maiduguri a yau;

Ko da shike shugaba Muhammadu Buhari, a yau zai kara gaba zuwa wata ziyarar Kai Tsaye a kasar UK idan ya gama hidimar sa a Jihar Borno a yau.

Karanta wannan kuma; An daga ranar Auren Adam A. Zango zuwa bayan Sallah

Shugaba Buhari zai yi wata ziyarar Kai Tsaye zuwa kasar UK

Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi wata tafiyar Ziyara ta kai Tsaye zuwa kasar UK a yau Alhamis, 25 ga Watan Afrilu 2019.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da shugabancin kasar ta bayar daga bakin Mista Femi Adesina, Mataimakin shugaban kasa wajen hidimar sadarwa.

A cikin bayanin Mista Adesina a birnin Tarayyar kasar Najeriya, Abuja, ranar yau Alhamis, ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kai tsaye zuwa kasar UK bayan rabuwan sa daga Maiduguri, Jihar Borno.”

Ya kara bayyana da cewa shugaba Buhari zai komo kasar Najeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu, gabacin ranar rantsarwa ga shiga shafin shugabancin kasa ta karo na biyu.

Wannan ziyar shugaban zuwa Borno da UK ya biyo baya ne bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai a Jihar Legas, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya.

A baya, Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Tsohon Shugaban Kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya gargadi tsohon ma’ikacinsa, Reno Omokri da ya nuna halin girmamawa da tarbi’a ga shugaba Muhammadu Buhari.

Omokri ya bayyana da cewa ya karbi kira daga tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan. Ganin dalilin da ya sa Jonathan yayi kirar, Omokri ya ce “Ban taba haduwa da Fasto, Liman ko wani Fafaroma ba da irin wannan halin girmamawa irin ta Goodluck Jonathan.” inji Reno.

#BokoHaram: Mutane 5 sun mutu, Kimanin 45 kuma da mugan raunuka a wata Kunar bakin wake

Kimanin mutane biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar harin ‘yan kunan bakin wake da aka yi a Maiduguri ta Jihar Borno a karshen makon da ta gabata.

Harin ta bar mutane kusan arba’in da biyar (45) da raunuka a yayin da ‘yan ta’addan suka hari wata shiyya da ake ce da ita Muna-Dalti, a garin Maiduguri, babban birni Jihar Borno, a daren ranar Asabar da ta wuce.

A ganewar Naija News, bincike ya bayyana da cewa ‘yan mata biyu ne suka aiwatar da kunar bakin waken.

An bayyana da cewa ‘yan kunar bakin waken sun hari shiyar Muna-Dalti ne da mugayan bama-baman (IEDs)  sanye a jikunan su a daren ranar Asabar.

Shugaban Hukumar (SEMA), Kachalla Usman ya gabatar ga manema labarai da cewa lallai harin da gaske ne, kuma mutane biyu sun mutu a yayin da ake nuna masu kulawa a Asibiti.

“A halin yanzu, ana kan bayar da kulawa ta gaske ga wadanda suka samu raunuka a sakamakon harin a babban Asibitin da ke a Maiduguri” inji Usman.

Karanta wannan kuma: Wani Mahaukaci ya Kashe Dan Sanda a Jihar Kwara

An gano wata ‘yar shekara 13 da Bama-Bamai a Jihar Maiduguri

An kame wata yarinya mai shekaru goma sha ukku (13) da aka gane da bama-bamai a Jihar Borno.

Rahoto ya bayar da cewa an kame yarinyar ne a kusa da rukunin Sojoji ta Giwa Barracks da ke a Maiduguri.

Bisa bincike, Naija News ta iya gane da cewa an kame yarinyar ne mai suna Zara, da mugayan Bama-Bamai ta (IED) sanye a jikinta. An kuma bayyana da cewa an samu kame yarinyar ne a yayin da ta fadi da gyangyadi nan kusa d mashigar rukunin sojojin yankin.

Da aka binciki Zara da bayanai, ta ce “An aiko da kimanin mutane goma sha hudu (14) sanye da bama-bamai zuwa yankin Bank da karamar hukumar Bama don kadamar da kunar bakin wake a Jihar Born”

“A halin yanzun an tafi da su cikin mota don ajiye kowani a inda ake bukatar tashin bam din, a cikin garin Maiduguri” inji Zara.

A halin yanzu an watsar da jami’an tsaro ko ta ina don bincike da kokarin dakatar da wannan mugun harin.

An kuma umurci al’ummar yankin duka da kasancewa a boye a gidajen su har sai an sami cin nasara da harin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Bam ya fashe a wata masallaci a Jihar Borno