Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli Bidiyon Obasanjo yadda ya bar Najeriya a gurguje bayan nasarar Buhari

Published

on

at

Kalli wata bidiyo da ta mamaye layin yanar gizo
Bidiyon na dauke da yadda tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, inda aka nuna shi a gurguje da kokarin barin kasar bayan nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben tseren kujerar shugaban kasa ta shekarar 2019.

Naija News ta gano wannan bidiyon ne a yayin da ‘yan Jam’iyyar APC da ke kasar Turai suka aika a layin twitter.
Kalli bidiyon a kasa;

Ka tuna a baya tsohon shugaban ya karyace zancen cewa ya gudu zuwa kasar turai bayan nasarar Buhari.

Obasanjo a bayanin sa da manema labarai a gidan sa da ke Abeokuta, Jihar Ogun da cewa karya ne jita-jitan da ya mamaye ko ta ina da cewa ya gudu zuwa kasar waje.

“Me zai sa in gudu daga kasar” inji Obasanjo a bayanin sa da manema labaran.

“Ko ba don komai ba, Daidai ne in tsaya in jefa kuri’a a matsayi na na dan kasar Najeriya ga zaben shugaban kasa da kuma ta gwamnoni da za a yi a watan Maris”

“Duk masu daukar wannan jita-jita ta karyan cewa na guje daga kasar; na bar su da Allah”