Connect with us

Labaran Najeriya

Kaito! Ga yadda wani ya kare da zaman rayuwa a kan layin Wutan Lantarki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta gano da rahoton wani matashi a yankin Eliozu, ta Port Harcourt, a Jihar Rivers da ya kone kurmus kan Falwayan Wutan Lantarki.

Bisa bincike da ganewa, matashin ya hau kan Falwayan ne da ke shiyar su ta Eliozu don gyara layin wutar su da ke da matsala.

Bisa bayanin wani mazaunin shiyar, ya bayyana ga manema labarai da cewa Matashin ya hau kan Falwayan ne don gyara wutar su ba tare da dama ko sanin Hukumar Samar da Wutan Lantarke ba.

“Ya hau kan Falwayan ne kwaram da kanshi ba tare da karban dama ko sanar da Hukumar Samar da Wutan Lantarke ba.” inji mutumin.

Ya kara da cewa Mutumin bai tuna da cire Fius na wutar ba daga Tiransifoma. “An mayar da wuta ne a yayin da matashin ke kan gyara wuta saman Fal. kuma daman bai tuna da cire layin fius na wutar ba, daga nan kawai sai hayakin kamun wutar muka gani har sai da ya mutu akan falwayan.”

Karanta wannan: An jera wa Wata Mari a yayin da abokiyarta ta gane ta da Soyayya da Tsohonta