Connect with us

Uncategorized

Miyetti Allah kungiyar Mahauta ne da ‘Yan Kisan Mutane – inji Fani Kayode

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Ministan Harkokin Jirgin Sama, Femi Fani-Kayode ya kalubalanci shugabancin kasa da kwatanta ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da wasu ƙungiyoyi masu halal kasar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kakakin shugaban kasa wajen sadarwan layin yanar gizo, Garba Shehu, ya bayyana cewa Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) kungiyar ce kamar Afenifere (Kungiyar Yarbawa) da kungiyar zamantakewar al’umman Iyamirai (Ohanaeze Ndi Igbo).

Shehu ya fadi hakan ne a zama tattaunawa da shugaban ‘yan sanda Najeriya, Mohammed Adamu yayi da Gidan Majalisar Dattijai akan matsalar tsaron kasar.

“Ba daidai ba ne a ce gwamnatin Najeriya na tattaunawa da ‘yan fashi” inji Garba Shehu.

“Kungiyar Miyetti Allah na kamar Ohanaeze da Afenifere ne. dukan su ƙungiyar zamantakewar kasa ne. Akwai ‘yan ta’adda a cikin ‘yan kabilar Yarabawa amma kuma ba za ku iya kiran Afenifere ‘yan ta’adda ba”

Jin hakan ne Mista Kayode, Jigo a Jam’iyyar Adawa, PDP ya mayar da martani ga zancen Garba Shehu na kwatanta Miyetti Allah da Afenifere da kuma Ohanaeze.

Kayode ya ce, “Ba haka bane, Miyetti Allah ƙungiyar Mayankan naman Saniya ne da kuma Mayankan Mutane. Su ‘yan tada zama tsaye ne, masu rikici da kuma masu kadamar da mugunta. Sun kasance da ƙyama kamar yadda suke da haɗari!” inji Kayode.

“Kwatanta Miyetti Allah da Afenifere ko Ohaneze kamar kwatanta Ikilisiyar Shaidan ne da Ikilisiyar tarayyar Angilika” inji shi.