Connect with us

Labaran Najeriya

Jam’iyyar HDP ta bukaci Kotu da dakatar da hidimar rantsar da Shugaba Buhari a ranar 29 ga Mayu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan sa’o’i kadan ga ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da shugaban Muhammadu Buhari da zama shugaban Najeriya a karo ta biyu, jam’iyyar siyasa mai suna Hope Democratic Party (HDP) ta yi kirar karar shugaban ga Kotun Koli. Jam’iyyar a kirar karar ta bukaci kotun ta dakatar da hidimar ranar 29 ga watan Mayu ga rantsar da Shugaba Buhari.

Aminiya ta sanar da rahoton cewa, HDP ta yi kira ga kotun ta da yin watsi da hukuncin Kotun Kasa game da gabatar da Shugaban kasar wadda kotun ta soke a baya.

Jam’iyyar adawar hade da dan takarar su, Ambrose Owuru, sun kalubalanci zaben watan Fabrairu 23, wanda ya bayyana cewa Buhari ne ya zama shugaban kasan Najeriya a karo ta biyu. HDP a cikin rokon su ta bukaci kotun ta hana shugaba Buhari da bayyana kansa don yin rantsarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Jam’iyyar sun kuma bada shawara da cewa Shugaban Gidan Majalisar Dattijai , Bukola Saraki ko kuma Babban Alkalin Kotun Tarayyar Kasa (CJN) ya maye gurbin shugaban har a magance matsalar da aka samu a hidimar zaben watan Fabrairu.

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli dalilin da ya sa aka hana Hidimar Sallar Durbar ta shekarar 2019 a Jihar Katsina.