Connect with us

Uncategorized

#Almajiri: An kama wani Malamin Almajirai da laifin yin Jima’i da ‘yan daliban sa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Malamin Makarantar Arabi

Rukunin ‘Yan Sandan Najeriya ta Jihar Sokoto ta kama wani Malam Murtala Mode, malamin makarantar Almajirai a garin Arkillan Magaji na jihar Sokoto da zargin cewa yana yin jima’i da yara shida da yake koyar da su a Jihar.

Malamin da aka kama shi, a cikin bayanin sa ya ce”Makoma na ne, nikan yi shi ne don samun kudi”

Da ake cikin jawabi a taron manema labarai a ranar Litinin, kwamishinan ‘yan sanda jihar, Ibrahim Kaoje ya ce a ranar 22 ga Mayu, 2019, Barrister Hamza Liman na hukumar kare hakkin Dan Adam ta kasa da kasa ya ruwaito da zancen malamin da ake zargin sa a ofishin ‘yan sandan Arkilla. A cewar Kaoje, Malamin ya amince da zargin da ake yi da shi wanda karya dokar kasa.

Daliban, ko da shike ba a gabatar da sunayen su ba, sun tsiro ne daga shiyar jihar Zamfara don karatun Arabi. Sun bayyana da cewa Malamin da ake zargi ya mayar da su kamar na’urar jima’i, kafin dada hukumar kare hakkin dan Adam suka zo ga kariyar su.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar ya ce’ zasu mayar da ‘yan makarantar ga iyayensu bayan an kammala binciken ga al’amarin. Ya kuma gargadi iyaye da su kauce wa aika yaransu zuwa makarantun Almajirai a wajen da ke nesa da su.

A halin yanzu, hukumar sun kuma gabatar da kama mambobin ‘yan banga shida da laifin sata da kadamar da cin zarafi.

KARANTA WANNAN KUMA; An kame wata Matar da Kokarin Shigar da Wiwi (Kayan Maye) a Gidan Yarin Jihar Kano.