Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 4 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 4 ga Watan Yuni, 2019
1. Shugaba Buhari ya karbi rahoto akan farfadar da SARS
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi rahoto daga hannun Hukumar Yanci ga Al’Ummar Kasa don farfado da sake tsarafa Hukumar SARS.
An bayyana cewa shugaban ya kuma bada goyon bayan kafa kwamiti don tattaunawa game da ayukan hukumar.
2. APC ta Jihar Zamfara sun kori Marafa da wasu mutane biyu kuma
Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu daga Jam’iyyar, akan laifin makirci ga Jam’iyyar.
Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar sun kori sanatan ne da ke wakilci a Zamfara Central a gidan Majalisa ta Takwas, hade da Hon Aminu Sani Jaji da kuma Mal Ibrahim Wakkala Liman.
3. Dalilin da ya sa Obasanjo bai amince da shugabancin Buhari ba – APC
Daya daga cikin Jigon Jam’iyyar APC, Cif kachi Iheme, ya kalubalanci tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo tare da Jam’iyyar Adawa (PDP), akan zargi da suke da cewa shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa na kokarin mayar da kasar Najeriya kasar Musulunci da kasar Fulani.
A bayanin Mista Iheme da manema labarai a kan wayar salula, ya fada da cewa Obasanjo na son ne kawai ya bata sunan gwamnatin Najeriya.
4. Rundunar Sojoji sun kashe Boko Haram 20 a shiyar Lake Chad
A wata ganawar rundunar sojojin Najeriya da ‘yan ta’addan Boko Haram, hadaddiyar rukunin sojojin ta Multinational Joint Task Force, sun bayyana cewa sun samu cin nasara da kashe ‘yan ta’adda 20 a shiyar Chadi.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a bayanin kakakin yada yawun jami’an tsaron, Col Timothy Antigha ya bayar da cewa sojoji hudu suka samu rauni a ganawar wutan.
5. An Jefa Tsohon Daraktan NIMASA a Kurkuru na tsawon shekaru 7
Tsohon Daraktan Maritime Administration and Safety Agency ta Najeriya (NIMASA), Callistus Obi zai je jarun shekara bakwai (7), ko kuma biyan kudi naira Miliyan N42m, bisa shari’ar kotun koli da ke a Jihar Legas.
Kotun ta gabatar da shari’ar ne a jagorancin Alkali Mojisola Olatoregun.
6. Boko Haram sun mamaye garin Borno
Naija News Hausa bisa rahotannai ta gane da zancen cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun mamaye Marte, hedikwatan karamar hukumar Marte, Jihar Borno.
Rahotannai sun bayar da cewa ranar Lahadi da ta gabata, Boko Harama sun fada wa rukunin sojoji ta Marte military base, 153 Task Force Battalion da harbe-harbe, suka kuma haska wuta a wuraren duka.
7. Hukumar INEC zata saki Takardan yancin wakilci ga Okorocha
Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC) sun bayyana da cewa za su bayar da takardan yancin wakilci a gidan Majalisar Dattijai ga tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, amma akan sharadi.
Wannan ya biyo ne bayan da Kotun neman yanci da ke a birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta bada dama don kafa baki ga karar da Okorocha ya gabatar da shi akan hukumar INEC a baya.
8. Sarkin Kano, Sanusi, ya bada Miliyan Biyar (N5m) don karban yancin ga wasu ‘yan gidan Yari
Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni da ta gabata, ya bayar da kudi naira Miliyan Biyar (N5m) don karban yancin wasu ‘yan gidan jaru da ke a gidan yarin Kurmawa da ta Goron, a nan birnin Kano.
A bayanin sarki Sanusi a lokacin da yake gabatarwa ga ‘yan gidan yarin da yake wa neman yanci, ya ce “Ina son ku gane da kuma daukar zama da rayuwar ku a gidan yari a matsayin nufin Allah, ina kuma gargadin ku da yin tunani mai zurfin don farfado da rayuwa mai kyau a yanzu da kuke batun samun yanci” inji mai Martaba.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com