Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 10 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 10 ga Watan Yuli, 2019
1. ‘Yan Shi’a sunyi Tawaye a gaban gidan Majalisar Dattijai, sun kone Motoci da barnan kayaki
‘Yan Kungiyar Shi’a sun lallace da kone wasu motocin da aka ajiye a gaban gidan Majami’ar Majalisar Dokokin Najeriya da ke a birnin tarayya, Abuja.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da yadda ‘Yan Shi’a suka kai zanga-zanga a gaban Ofishin Majalisar Dattijai, a ranar Talata da ta gabata, inda har aka rasa rayuka da dama.
2. Dubi Kuri’un da Atiku da Jam’iyyar PDP ke gabatarwa a Kotun Kara don kalubalantar nasarar Buhari
Shaidu sun fito a ranar Litinin da dama a yayin da jam’iyyar PDP da dan takaransu a zaben shugaban kasa na Fabrairu 23, 2019, Alhaji Atiku Abubakar ke kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari akan zaben.
Ka tuna a baya da cewa Atiku da PDP sunn kalubalanci hukumar INEC akan nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa Jam’iyyar APC.
3. Majalisar Dattijai bayyana zancen kisa ga Masu yiwa mutane Fyaden dole
A ganin yanayin yadda fyaden dole ke yaduwa a kasar Najeriya, Majalisar Dattijai, a ranar Talata ta gabatar da zancen bada hukunci kisa ga duk wanda aka kara gane da irin wannan laifi.
Hakan ya bayyana ne a yayin da Sanatan da ke wakiltar yankin Arewacin Jihar Cross River, Sanata Rose Oko, yake gabatarwa da yin kula da yadda ake karuwa da halin fyaden dole a kasar.
4. ‘Yan Majalisa su daga zaman su saboda zanga-zangar ‘yan Shi’a
‘Yan majalisar wakilai sun hanzarta da dakatar da zamansu a ranar talata da ta gabata, bayan da mambobin kungiyar musulunci ta Nigeria (IMN) da aka sani da shi’ yan Shi’ah suka shiga cikin majalisar da zanga-zanga.
Kakakin yada yawun Majalisar, Femi Gbajabiamila ya shaida wa Majalisar da cewa ya zan dole su dakatar da zaman saboda matsalar tsaro, a yayin da ‘yan Shi’a suka mamaye kewayan.
5. Atiku/Buhari: An ba mu wata lambar Asiri don Bayyana Sakamakon zabe a na’ura – inji Jami’in Hukumar INEC
An gabatar ga Kotun Koli na Kasa da ke jagorancin karar zaben Shugaban kasa a Abuja, a bayanin wani ma’aikacin hukumar INEC ga hidimar zaben watan Fabrairu, Ogunsanya Abiola, a ranar Talata da cewa anki bayyana sunan na’urar kwanfuta da aka ajiye sakamakon zaben shugaban kasa ta 2019.
Abiola, a yayin da yake magana a kotun ya bayyana cewa hukumar kawai ta ba su wata lambar sirri ne da za su iya samun dama ga shiga kwanfutar.
6. Buhari ya sadu da Baru da kuma Kyari a wata ganawar kofa kulle a Aso Rock
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya gana da Maikanti Baru da Melee Kolo Kyari a wata tattaunawar daki kulle a nan fadar shugaban kasar, a Abuja.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Baru shi ne Babban Darakta Janar na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC), a da, a yayin da Kyari ya maye gurbin shi kuwa a yanzu.
7. Atiku ya kada Shugaba Buhari a zaben Jihar Katsina – Jam’iyyar PDP
Ciyaman Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina, Salisu Maijigir, ya shaida wa Kotun Karar zabe a Abuja da cewa, Atiku Abubakar ya lashe zaben Shugaban kasa bisa yawar kuri’u fiye da Muhammadu Buhari a Jihar Katsina, a lokacin zaben shekarar 2019.
Salisu ya bayyana hakan ne a yayin da PDP da Atiku ke kalubalantar nasarar Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe a shekarar 2019.
8. Shugaba Buhari ya amince da inganta wasu takwarorin Jarumai da shugaban rundunar Sojoji
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kara inganta wasu manyan jami’an sojan Najeriya.
A wata sanarwa da Col. Sagir Musa ya bayar, a ranar Talata 9 ga watan Yulin da ya gabata, ya ce shugaba Buhari ya kara ingata Janar LO Adeosun, Babban Jami’in Koyarwa da Tsaro a hedkwatar sojojin kasar, ya kai ga mukamin Lieutenant-Janar.
9. Janar Tukur Buratai ya saura da matsayin babban jami’in sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da aka bayar da cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dakatar da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Lt-Gen Tukur Buratai daga ofishin sa.
Rashin fahimtar ya yadu ne bayan da Col. Sagir Musa ya sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ingata Babban Daraktan Rundunar Sojoji a tsaro da koyaswa, Major Janar LO Adeosun, da kara masa matsayi zuwa ga mukamin Lieutenant-Janar.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com