Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na batun karban Haraji Akan Kayan Lemu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yayin kokarin yawaita hanyar shigar da kudade a kasa, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fito da sabon tsarin sa biyan haraji kan kayan lemu iri-iri da ake sha a kasar.

Naija News ta fahimci cewa Ministar Kudi ta Najeriya, Misis Zainab Ahmed wacce ta sanar da hakan ta ce gwamnatin tana aiki kan yadda za ta kara inganta hanyoyin samun kudade a kasar.

Da take karin bayani yayin taron shekara-shekarar na Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya, Zainab ta bayyana cewa gwamnatin tarayya tana kokarin karfafar ne da GDP na kasar daga kashi bakwai zuwa takwas din kashin GDP 15.

Malama Zainab ta jadada da cewa za a zartar tsarin kudirin kasafin kudin tare da kasafin shekarar 2020 ga Majalisa da fatar cewa za a amince da hakan don karfafa kasafin kudin shakarar.