Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Duk Fim Da Ba Sakon Kwarai, Kyal-kyal banza ne kawai – Inji Sani Mu’azu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Kwararre a shafin shirin fim da kuma tsohon darekta, Sani Mu’azu, a cikin wata sako da ya aika a shafin yanar gizon nishadarwa tasa na Twitter, ya gargadi ‘yan shirin fim akan ire-iren fim da ake shiryawa.
Mu’azu a cikin  bayanin nasa ya bayyana da cewa shirya fina-finai don nishadantarwa kawai, kyal-kyal banza ce kawai idan har babu wata sako mai karfi a cikinta.
“Yin film don nishadantarwa kawai, kyal-kyal banza ne kawai idan babu wani sako mai Karfe.”
“Ga wanda ya jahilci abun,harkar film kamar kwalba ce. Za a iya amfani da ita wajen bayar da ruwa ko magani. Za kuma a iya amfani da ita wajen sayar da giya. A iya sani na, duk film din da bai dauke da wani sako da zai inganta rayuwa to fanko ne,” inji Mu’azu.
Ga sakon a kasa kamar yadda ya rabar;