Labaran Najeriya
Kada Ku Bar APC ta Rushe Bayan Wa’adina – Sakon Buhari Ga Shugabannin Jam’iyyar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi shugabancin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) kan tabbatar da cewa Jam’iyyar ba ta rusheba bayan ya karshe wa’adinsa a shekarar 2023.
Da shugaban yake jawabi a wurin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar a Abuja, ranar Juma’a, ya kara da cewa Jam’iyyar za ta zama tarihi ne kawai idan har ta iya kasancewa da karfi kuma tana da matukar kulawa da talakawa.
“Manufar ita ce, kamar yadda na fada a jiya, tarihi ba zata yafe mana ba idan APC ta rushe a karshen wannan wa’adin. Amma Tarihi zata amince da adalcinmu idan har jam’iyyar APC ta ci gaba da karfi, ba wai kawai ta rike cibiyar ba amma ta samu nasarori. Mutane za su yi tunani tare da nazari kwarai da gaske cewa da shugabannan da suka kafa APC sun yi sadaukarwa da yawa, sun kuma yi aiki tuƙuru.” inji Buhari.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Tsohon Ministan Sufuri, Kayode Ya Kalubalanci Ahmed Lawan kan Zancen Shugaba Buhari.
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama a karkashin Gwamnatin Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode, ya bayyana majalisar dattawan Najeriya a jagorancin Ahmed Lawan a matsayin taron tawul.
Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman Shugaban Majalisar Dattawar cewa duk wata bukata daga Shugaba Muhammadu Buhari abu ne mai kyau ga kasar Najeriya.