2016NPOWER: Dalilin Jinkiri Da Biyan Albashin N-POWER Na Watan Aktoba da Nuwamba

Ministan ba da agaji, kula da bala’i da ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq ta bayar da bayani kan dalilin da ya sa har yanzu ba a sami biyan albashin watan Aktoba da Nuwamba ga masu aikin N-Power ba.

A cikin bayanin da ta gabatar, har yanzu ba a biya albashi din ba saboda wadanda suka yi rajista a shekarar 2016 ba su fice daga hidimar N-Power din ba.

Mallam Sadiya ta fadi hakan ne a ranar Litinin yayin da take zantawa da manema labarai a birnin tarayyar kasa, Abuja.

Ta ce yakamata a ce wadannan masu amfana da hidimar N-Power tun karo na farko sun kai ga karshe wa da kuma isa ga manyan kamfanoni don karin inganci.

“Na samu rubutattun bayanan farko daga shugabannin hukumomin da shirye-shiryen gabatarwa daga ma’aikatar tun watan Oktoba na 2019. Duk akan gwagwarmaya da wahala da akwai cikin tafiyar da hidimar, a yayin da mika ragamar ke kan gudana” inji Sadiya.

“Game da korafe-korafe da kokawa da ba su dace ba game da rashin biyan albashi na watan Oktoba da Nuwamba na 2019 ga masu cin damar aikin N-Power, ma’aikatar na son ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da cewa masu cin damar shirin SIPs din sun samu zarafi mai dacewa akan ƙa’idodin aikin.” 

“Wadanda ke cin damar hidimar N-Power da suka yi rajista a shekara ta 2016 har yanzu ba a fice ba daga shirin, harma watanni 16 bayan karshe kwantiraginsu. Ya kamata su kammala hidimarsu don samun kyakkyawan inganci a gaba.”

“A yanzu haka ma’aikatar tana kokarin kirkirar dabarun ficewarsu, wacce babu shirin haka tun a farko.”

Kodashike, Naija News a baya ta ruwaito da cewa Maryam Uwais, mai ba da shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkar saka jari ta ce an riga an sanya shirye-shiryen ficewa ga masu cin damar aikin N-Power wadanda lokacin hidimar tasu ya kare ko.

Malama Maryam ta fadi hakan ne yayin da take zantawa da manema labaran NAN a ranar Litinin.