Connect with us

Uncategorized

Ba Zan Sake Neman Matsayi Ba a Zaben Najeriya – Inji Danjuma Goje

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Muhammad Danjuma Goje, ya sanar da aniyarsa na janyewa daga kara tsayawa takara a nan gaba.

Tsohon gwamnan jihar Gombe din ya bayyana hakan ne a yayin wata hidima mai taken ‘Goje Empowerment Programme’ wadda ya gudana a filin wasa na Pantami a Gombe.

Duk da haka, Goje ya ce zai ci gaba da taka rawar gani a fagen siyasar jiha da na kasa baki daya.

“Bayan na yi takara kuma na ci nasara a dukkan zabubbuka bakwai, kari da kasancewana Ministan kasar, na yi imanin cewa Allah (SWT) ya yi mini alheri. Na yi imanin cewa ‘yan Najeriya da yawa ba su samun irin wannan damar ba” in ji Goje.

“Bayan kawo ga tsufa na, ina mai sanar da ku cewa na yanke shawarar janyewa daga sake tsayawa takara. Don nisantar shakku, ba zan fita neman takara ba a kowane irin zabe ko mataki ba.”

“Duk da haka, wannan baya nufin cewa zan yi ritaya daga siyasa ba; ba haka bane. Zan ci gaba da kasancewa da aikin siyasa a karkashin ja’iyyar APC. Da kuma in shiga cikin dukkan harkokin siyasa a kowane matsayi, amma dai ba zan tsaya takara ba.”

“Na samu dama mara matukar dace na yin takara tare da cin zabe har sau bakwa.