Uncategorized
FRSC: Hadarin Mota Ya Kashe Mutane 12 a Neja
Hukumar kiyaye haddura ta tarayya (FRSC), a jihar Neja ta bayyana cewa mutane 12 ne suka mutu a wani hadarin mota da ya faru a ranar Lahadi a kauyen Sawmill da ke kan hanyar Mokwa zuwa Makera, a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Kwamandan Rundunar FRSC a yankin jihar, Mista Joel Dagwa, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litinin a Minna cewa hatsarin ya faru ne da wata motar da ke dauke da rajista mai lamba KJ 555 XX, akan hanyarta zuwa Legas.
Dagwa a cikin bayaninsa ya ce motar da ta zo daga Maiduguri, ta dauki fasinjoji ne daga Zariya a cikin jihar Kaduna kafin ta nufi birnin Legas.
“Hadarin ya shafi mutane 103; Mata 55, maza 40, 8 yara. 12 daga cikinsu sun mutu yayin da 91 suka samu raunuka amma dai an kai su babban asibiti na Mokwa don yi musu magani.”
Ya kuwa danganta hadarin motar da yawar gudu daga hannun direban motar.
Kwamandan sashen yayi jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da sa ido kan matafiya akan hanyar don kiyaye yawar lodi da tuki mai hadari.
“Tun daga wannan lokacin mun fara zirga-zirgar yawon bincike da kula da tafiye-tafiye a dukkan manyan hanyoyin domin tabbatar da cewa masu amfani da titin sun bi ka’idodin zirga-zirgar ababen hawa da kiyaye ka’idodin titi kafin, lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.” in ji shi.