Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Biliyan N148b

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Talata (yau), 10 ga watan Disamba 2019, gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan N148b na shekarar 2020.

Gwamna Bello, yayin gabatar da kasafin kudin ga Majalisar Dokoki ta Jihar a Minna, babban birnin jihar Neja, ya ce kasafin kudin shekarar 2020 da aka yiwa lakabi da ‘Kasafin Kuɗi don Ci gaba Mai ɗorewa’, zai kasance ne kan tabbatar da kammala dukkan ayyukan da ke gudana a jihar, da kuma ƙudirin cewa gwamnatinsa bata bar kowace aiki ba a sake.

Kasafin kudin ya kasance ne sama da biliyan N69b domin kashewa ga ayukan da ke a baya da kuma biliyan N78b  domin manyan ayuka na musanman a jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa za a samar da kudaden ne ta hanyar haraji da ke shigar asusun jiha, Asusun Kwamitin Tarayyar (FAAC) da sauran hanyoyin samun kudaden da gwamnatin jihar ke da ita.

Gwamnan ya ba da fifikon wasu ayyukan da aka aiwatar karkashin kasafin kudi na shekarar 2018 don hada da sake fasalin wasu hanyoyin karkara da biranen jihar; sayen motocin bas don bunkasa ayyukan sufuri a jihar.

A cewarsa, Jihar Neja ta hada hannu da Bankin Duniya don gyara ma’aikatar Moribund Ladi Kwali Pottery, a yanzu kuma an riga an kashe kimanin Naira Miliyan N45m, inji shi.

Haka kuma, an kashe sama da Naira Miliyan 100 don gyara Makarantar Kwararrun Malaman, watau ‘Teachers Professional Institute’ wacce ke a karamar hukumar Shiroro, da kuma sake gina dakin karatun kwamfuta, ICT/E-Library ta Cibiyar Justice Fati Lami a kan kudi Naira Miliyan N17m.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Yobe Ya Dakatar da Wani Hakimi a Kan Laifin Lalata Da Wani Yaro Dan Shekara 6

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba da umarnin dakatar da shugaban gundumar Fannami, Lawan Mari daga karamar hukumar Bade saboda zargin yin lalata da wani yaro dan shekara shida.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Harkokin Cikin gida da Al’adu, Abdullahi Bego, ya ce gwamnan ya ba da umarnin gaugawa da a dakatar da shugaban gundumar.