DSS: Osinbajo Ya Mayar Da Martani Game Da Sake Kamun Sowore

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya mayar da martani game da batancin da aka yi a babbar kotun tarayya a Abuja, a kokarin sake kama Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow.

Da mataimakin shugaban kasar ke tsokaci kan sake kama Omoyele Sowore, bayan da ya yi watsi da kyauta karramawa daga Cibiyar Nazarin Labarai ta Wole Soyinka, Osinbajo ya nuna takaicin ayyukan ‘yan sanda asirin kasar, watau hukumar DSS.

Naija News ta fahimci cewa Mataimakin Shugaban wanda ya kasance jigon mai magana a wata taron Hadaddiyar Daular Larabawa da aka yi, ya yi bayani a cikin wata sanarwa da kakakin yada yawun sa Laolu Akande, ya bayar da cewa Mataimakin shugaban ya ki karbar kyautar karramawa din da aka shirya masa na taka rawar gani a lokacin da yake jagoranci a jihar Legas ne saboda lamarin da ya gudana ranar Juma’a da ta gabata, akan sake kame Sowore.

Ya ce “A gani na zai zama rashin hankali ne da kuma rashin daidaituwa idan na halarci bikin Wole Soyinka, musanman karban karramawar a halin da ake a ciki.”

Bayan hakan Osinbajo ya bayyana murna da gode wa wadanda suka shirya taron, musanman da shirya masa kyautar. Cibiyar, ta kuma ba da sanarwar, da farko da cewa ta dakatar da bayar da karrama ga mataimakin shugaban akan cewa “bai dace da kyautar ba” a wannan lokaci da yanayin da ake a ciki.