Labaran Najeriya
Osinbajo Da Gwamnonin Jiha Na Taron NEC Ta Karshe A Shekarar 2019
0:00 / 0:00
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a yau Alhamis, 19 ga watan Disamba 2019 ya jagoranci taron Kwamitin Tattalin Arzikin Kasar (NEC).
Naija News ta tattaro da cewa gwamnonin jihohi sun halarci taron wanda ya fara gudana da misalin karfe 11:06 na safe.
Taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, shi ne taro na karshe ta NEC wadda za su yi a shekarar 2019.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 a cikin doka.
Shugaban ya rattaba hannu ne ga kasafin kudi Naira miliyan 10.5 a ofishin fadar Shugaban kasa, Abuja.
© 2024 Naija News, a division of Polance Media Inc.