Osinbajo Da Gwamnonin Jiha Na Taron NEC Ta Karshe A Shekarar 2019

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a yau Alhamis, 19 ga watan Disamba 2019 ya jagoranci taron Kwamitin Tattalin Arzikin Kasar (NEC).

Naija News ta tattaro da cewa gwamnonin jihohi sun halarci taron wanda ya fara gudana da misalin karfe 11:06 na safe.

Taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, shi ne taro na karshe ta NEC wadda za su yi a shekarar 2019.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 a cikin doka.

Shugaban ya rattaba hannu ne ga kasafin kudi Naira miliyan 10.5 a ofishin fadar Shugaban kasa, Abuja.

Kasafin Kudin 2020 Zai Taimaka Wa Najeriya Zuwa Ga NEXT LEVEL – Osinbajo

Shugaba Muhammadu Buhari ya samu yabo da karramawa daga Mataimakin sa, Yemi Osinbajo, kan saurin sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 zuwa doka.

Kamfanin dilancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Shugaba Buhari a ranar Talata, ya rattaba hannu kan kasafin kudi ta 2020 zuwa doka a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Ka tuna da cewa Mataimakin shugaban kasar ya halarci lokacin rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban ya gabatar a fadar gwamnati.

Osinbajo yayin da yake magana kan kudirin dokar ya lura cewa kasafin kudin zai taimaka ga bunkasa kasar zuwa gaba.

Osinbajo wanda ya sanya a shafin sa na Twitter ya rubuta cewa, “Sa hannu a kasafin kudin shekarar 2020 a yau, Shugaba Buhari ya maido da tsarin watan Janairu zuwa Disamba.”

“Kasafin kudin zai taimaka ga bunkasar ayyuka “zai ciyar da kasar mu ga ci gaba yayin da muke zuwa Next Level.”

DSS: Osinbajo Ya Mayar Da Martani Game Da Sake Kamun Sowore

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya mayar da martani game da batancin da aka yi a babbar kotun tarayya a Abuja, a kokarin sake kama Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow.

Da mataimakin shugaban kasar ke tsokaci kan sake kama Omoyele Sowore, bayan da ya yi watsi da kyauta karramawa daga Cibiyar Nazarin Labarai ta Wole Soyinka, Osinbajo ya nuna takaicin ayyukan ‘yan sanda asirin kasar, watau hukumar DSS.

Naija News ta fahimci cewa Mataimakin Shugaban wanda ya kasance jigon mai magana a wata taron Hadaddiyar Daular Larabawa da aka yi, ya yi bayani a cikin wata sanarwa da kakakin yada yawun sa Laolu Akande, ya bayar da cewa Mataimakin shugaban ya ki karbar kyautar karramawa din da aka shirya masa na taka rawar gani a lokacin da yake jagoranci a jihar Legas ne saboda lamarin da ya gudana ranar Juma’a da ta gabata, akan sake kame Sowore.

Ya ce “A gani na zai zama rashin hankali ne da kuma rashin daidaituwa idan na halarci bikin Wole Soyinka, musanman karban karramawar a halin da ake a ciki.”

Bayan hakan Osinbajo ya bayyana murna da gode wa wadanda suka shirya taron, musanman da shirya masa kyautar. Cibiyar, ta kuma ba da sanarwar, da farko da cewa ta dakatar da bayar da karrama ga mataimakin shugaban akan cewa “bai dace da kyautar ba” a wannan lokaci da yanayin da ake a ciki.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 10 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 10 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Masar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata, 10 ga Disamba, 2019, ya bar Najeriya zuwa Aswan, kasar Egypt, don halartar taron Aswan.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an tsara dandalin ne don kawo Cigaba ga Afirka.

2. Dalilin da yasa Ban halarci Shirin Kyautar Soyinka ba – Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya dora laifin a kan ci gaba da tsare Omoyele Sowore, mai wallafa labarai ta yanar gizo na Sahara Reporters, cewa saboda wannan ne ya sa ya ki zuwa Cibiyar Nazarin Bincike ta Wole Soyinka.

Naija News ta fahimci cewa ya kamata a karrama Osinbajo ne da lambar yabo a wannan hidimar saboda rawar da ya taka a aikin tabbatar da adalci a jihar Legas, yayin da ya kasance kwamishinan jihar da kuma Attorney General.

3. Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Shugaban FIRS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Muhammad M. Nami a matsayin sabon shugaban hukumar ‘yan rebenu ta Tarayya (FIRS).

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, an bayyana nadin Nami ne a cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Litinin bayan da Garba Shehu, Babban mai ba da shawara na musamman kan harkar yada labarai ga Shugaban kasa ya sanar da hakan.

4. Zaben Kogi: Natasha Ta Gabatar Da Karar Rashin Amince Da Zaben Bello a Kotu

‘Yar takarar kujerar gwamna a jihar Kogi a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba 2019, Natasha Akpoti, ta tunkari kotun kolin zabukan gwamnoni kan sakamakon zaben.

A cikin takardarta, Barr. Akpoti ta shigar da kara a gaban kotun a ranar Asabar da daddare, na neman a soke zaben.

5. Sarautar Tinubu Ya Kare, Sowore A Yanzu Shine Sabon Shugaban Yarbawa – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce zamanin Bola Tinubu a matsayin jagora a kasar Yarbawa ya kare saboda Omoyele Sowore, jagoran kungiyar #RevolutionNow, a yanzu shine sabon shugaban Yarbawa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, Kanu ya yi wannan bayanin ne yayin wata faifan rediyo a gidan Rediyon Biafra a ranar Lahadi, 8 ga Disamba, inda ya yi magana kan cin zarafin Sowore da jami’an DSS suka yi da kuma cin zarafin bil adama a Najeriya.

6. 2023: Arewa Ta Bada Buqatar Da Zai Sa Su Mikar da Shugabanci Ga Kudu

Wata kungiyar Matasan Arewa ta yi gargadi game da shirin yankin na mika mulki ga Kudu a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kare wa’adinsa a shekarar 2023.

Dangane da bayanin matasan da ke gudana a karkashin kungiyar Arewa Youths Consultative Forum, AYCF, sun ce cin mutuncin ‘yan Arewa da ake yi a Legas daga hannun kungiyar Task Force na sa Arewa matukar yin nazari kan mikar da kujerar shugabanci ga kudu.

7. Miliyoyin ‘Yan Najeriya Ba Su Damu Da Sake Kamun Sowore Ba – Femi Adeshina

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa miliyoyin ‘yan Najeriya ba su damu da batun sake kamun Sowore da ma’aikatar Tsaro ta sake yi ba a babbar kotun tarayya a makon da ya gabata.

Adesina ya bayyana hakan ne a shirin Tashar Talabijin ta Channels a ranar Litinin lokacin da aka nemi ya bayyana matsayin sa game da mamaye Kotu don kamo Omoyele Sowore.

8. Muna Zantawa Buhari Kan Yanayin El-Zakzaky – Gwamnatin Iran

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa tana cikin tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, IMN, da aka fi sani da ‘Yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Abbas Mousavi, ya ce kasar tasu ta hanyar diflomasiya, tana hulda da gwamnatin Najeriya kan yanayin halin da El-Zakzaky ke a ciki.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a koyaushe a Naija News Hausa

Shugaba Buhari Na Ganawa Da Oshimhole, Manyan ‘Yan APC Don Hana Rushewar Jam’iyyar Bayan Wa’adinsa Ta 2

Buhari Ya Zarta Da Manyan Shugabbanai A APC Kan Rikicin Da Ke Gudana a Jam’iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau jumma’a, 6 ga watan Disamba 2019 na ganawa da Shugaban Jam’iyyar APC kan neman zabe na kasa, Adams Oshiomhole kan rikicin da ke ta karatowa jam’iyyar da ke shugabanci.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Shugaba Buhari a ranar Alhamis ya gana da gwamnonin APC a Fadar Shugaban kasa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wannan dandali na labarai ta yanar gizo ta fahimci cewa gwamnonin jam’iyyar APC sun halarci taron ne a jagorancin Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, arewa maso-yammacin Najeriya.

Taron kuwa ta samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Shugaban Ma’aikata ga Shugaban, Mista Abba Kyari.

Koda yake, shugaban jam’iyyar APC na kasa da ake bukatar bayyanarsa a taron bai samu hallararta ba.

An tattaro cewa Oshiomhole a yau zai gana da Shugaba Buhari, tare da shugabannin jam’iyyar na kasa.

Wani babban jigo a jam’iyyar APC ya fada wa jaridar The Punch da cewa, “ganawar ta biyu wani bangare ne na kokarin kawar da rarrabuwar kawunan ‘yan jam’iyyar bayan wa’adin shugaba Buhari na biyu.

Wani abokin aiki da Oshiomhole ya bayyana cewa tsohon gwamnan, Oshiomhole, bai karbi gayyata kan taron jam’iyyar APC ba wacce ta gudana a ranar Alhamis, saboda haka bai kamata a yi tsammanin hallararsa ba a taron.

“Taro ne da gwamnonin APC suka yi don haka bai kamata shugaban jam’iyyar ya halarci taron ba. Gobe dai (Juma’a) zai jagoranci manyan shugabannin jihohi don ganawa da Shugaban kasar,” inji shi.

Naija News Hausa ta fahimci cewa wannan itace taron farko da shugaba Buhari zai yi da Ciyamomin jam’iyyar ta jiha tun bayan babban zaben 2019.

Shugaba Buhari Na Ganawar Siri da Majalisar Zartarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocin kasar suna halartar taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako da mako a Abuja.

Naija News ta gane da cewa Taron na gudana ne a zauren majalisa na fadar Shugaban kasa.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha suma sun halarci taron.

An bayyana da cewa taron sirin ya fara ne jim kadan bayan bude taro da addu’a daga bakin Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola, da Ministan Harkokin Wajen, Mista Geoffrey Onyeama.

A cikin wata sanarwa da Naija News Hausa ta ruwaito a baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi shugabancin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) kan tabbatar da cewa Jam’iyyar ba ta rusheba bayan ya karshe wa’adinsa a shekarar 2023.

Da shugaban yake jawabi a wurin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar a Abuja, ranar Juma’a, ya kara da cewa Jam’iyyar za ta zama tarihi ne kawai idan har ta iya kasancewa da karfi kuma tana da matukar kulawa da talakawa.

2023: Ga Takaitaccen Hirar Tarayyar APC da Shugaba Buhari ya jagoranta

Shugaban hidimar neman zaben Jam’iyyar APC na ƙasa, Comrade Adams Oshiomhole, Da yake jawabi bayan taron wanda ya ƙare da misalin ƙarfe 11:30 na yammacin ranar Alhamis, ya ce batutuwan da aka tattauna yayin taron daren jiya sun haɗa da aiwatarwa a zaɓen da suka gabata, batutuwan yau, kasafin kuɗi, shari’ar kotu, da kuma batun ladabtarwa.

Oshiomhole ya ce, “Kun san wannan ganawar ta tarayyar jam’iyyar ne. Ainihin, taron ya kasance ne kawai don nazarin ayyuka a zabukan da suka gabata, abubuwan da suka shafi yau, kasafin shekara mai zuwa, da batutuwan horo. Kun san rukunin APC din kamar majalisar dattawa ne don yin magana kan abubuwa da yawa waɗanda zamu tattauna a NEC a gobe (watau a yau).”

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa wanda ya yi maganansa ta karon farko bayan furucin Darakta Janar na kungiyar ci gaban Gwamnonin (PGF) Salihu Mohammed Lukman kan yadda yake tafiyar da jam’iyyar, ya yi watsi da kalaman da Lukman ya yi.

“Babu matsin lamba. An shirya taron NEC kamar watanni biyu da suka gabata. Muna jiran kawai ranar ta zo ne. An sanar da shi ne watanni biyu da suka gabata. Kuma za a gudanar da shi ne a gobe (watau yau). Shin ba ku san da wannan ba?”

“Kana maganar abin da Mista Salihu Lukman ya fada, Wannan shine ra’ayinsa. Tun ma kafin ya fadi haka, an shirya wannan ganawar. Ba daidai bane a gudanar da taro,” in ji shi.

“Muna da taron NEC don duba bayanan asusunmu na shekarar da ta gabata, kasafin kudin shekara mai zuwa, matsalolin da suka taso lokacin zabuka da kuma bayan zabuka, da kuma sakamako daban-daban da suka shafi kotu; wanda muka ci nasara da wanda muka rasa; ci gaba; al’amurra a wasu jihohi inda muke da sabani da kuma yadda za mu warware rashin jituwa. Ina tsammanin haka ne. Kuma taron ya gudana yadda ya kamata. Kuma za ka iya ganin shugaban kasan a zaune har karshen taron.” Inji Oshiomhole.

Buhari Ya Shugabanci Taron FEC na farko bayan Dawowa daga Kasar London

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yau Laraba, 20 ga watan Nuwamba ya jagorancin taron Majalisar zartarwa ta tarayya wanda ya kasance taron farko bayan dawowar sa daga kasar Landan.

Naija News Hausa ta fahimci cewa taron da ake yi a birnin Tarayya, Abuja, itace zaman shugaban na farko bayan dawowa daga ziyarar da shugaban ya kai a Burtaniya.

Ka tuna da cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron na FEC a lokacin da Buhari ya ke a can burtaniya a ziyarar kwanaki 15 da ya tafi.

Rahoto ya bayyana da cewa Osinbajo tare da wasu ministocn kasar da dama sun halarci a taron da ake a yau.

Kamin aka kafa kai ga taron, anyi juyayi na ‘yan mintuna don girmama tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Marigayi Mista Ufot Ekaette, da wani tsohon Ministan Yada Labarai, Marigayi Cif Alex Akinyele.

KARANTA WANNAN KUMA; Ba na Tsoron Mutuwa – inji Tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 13 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 13 ga Watan Nuwamba, 2019

1. An gabatar da Dokar Kalaman Kiyayya a gaban Majalisar Dattawan Najeriya a karo ta Farko

A kokarin magance matsalolin da ake samu daga wasu masu amfani da kafofin yada labarai don yada kalaman kiyayya da baci, Majalisar Dattawan Najeriya ta sake gabatar da Dokar ‘Kalamun Kiyayya’ a zauren Majalisar Dokokin kasar.

Naija News ta fahimci cewa ranar Talata da ta gabata ne karo na farko da majalisar dokoki ke kafa baki ga zanecen dokar, don kafa wata hukuma da za ta hana maganganun kalaman nuna kiyayya.

2. Hukumar DSS Sun Yi Harbe-harbe a A Lokacin da ake Zanga-zangar a saki Sowore

Ma’aikatar hukumar tsaron kasa (DSS) a ranar Talata, sun harba tiyagas don tarwatsa masu zanga-zanga da suka afka wa ofishinta don neman sakin Omoyele Sowore.

Masu zanga-zangar, a karkashin jagorancin Deji Adeyanju, sun mamaye ofishin hukumar ne a Abuja domin neman a saki Sowore nan da nan.

3. Shugabannin Jam’iyyar APC Sun Fitar da Gargadi Akan Gwamnan da ake Amfani da shi Don Tsanantawa Osinbajo

Wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke a Amurka sun yi zargin cewa akwai wata rukuni a cikin Aso Rock da ke amfani da wani Gwamna na Kudu maso Yamma, don tsananta wa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Sun kara da zargin cewa Rukunin suna amfani da gwamnan ne wajen lalata da raunana matsayin Osinbajo domin hana shi fita takarar shugabancin kasar a shekarar 2023.

4. Yahaya Bello ya Bada Hutun Aiki ga Al’ummar Jihar Kogi don Zaben Ranar Asabar

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayar da hutu ga mai’aika, ‘yan makaranta da al’umar jihar domin hidimar zaben tseren kujerar gwamna da za a yi a jihar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba 2019.

Gwamna Yahaya Bello ya amince da ranar juma’a, 15 ga Nuwamba a matsayin ranar hutu ta jama’a da dukkanin makarantun da ke jihar.

5. Matasan Arewa sun Dage da cewa ba Shugaba Buhari ne ke Shugabancin Kasar ba

Shugaban kungiyar, Arewa Youth Consultative Forum (AYCF), Yerima Shettima ya ayyana da cewa ba Shugaba Muhammadu Buhari ba ne ke tafiyar da mulkin kasar.

Naija News ta tuno da cewa Buhari ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata cewa shi ne ke jagorancin kasar, ba kuwa shugaban Ma’aikata, Abba Kyari ba.

6. 2020: Ize-Iyamu Ya Shirya da Barin PDP zuwa APC

Tsohon mai neman kujerar gwamna a jihar Edo a shekarar 2016, Fasto Osagie Ize-Iyamu ya yi batun barin jam’iyyar sa da komawa jam’iyyarsa APC.

Naija News ta tuno cewa dan takarar gwamna a karo na biyu na Jam’iyyar PDP, Ize-Iyamu ya tsaya takarar gwamna a jihar a 2012 da 2016.

7. Sowore: An Ba mu N1m don Dakatar da Zanga-Zanga – Adeyanju

Wakilin kungiyar ‘Concerned Nigerians’, Deji Adeyanju, a ranar Talata, ya bayyana da cewa wasu masu goyon bayan gwamnati sun baiwa kungiyar kudi miliyan N1m don su dakatar da zanga-zangar adawa da suke yi kan tsare Omoyele Sowore da aka yi.

Adeyanju ya bayyana hakan ne yayin zanga-zangar da ke gudana a hedikwatar DSS da ke Aso Drive a Abuja, babban birnin kasar.

8. Zaben Kogi: Dino Melaye ya fitar da sunayen ‘Yan PDP 27 da’ Yan Sanda za su kama

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Kogi West a majalisar dattijan Najeriya, ya yi zargin cewa rundunar ‘yan sandar Najeriya (NPF) ta na da shirin ta kama membobin kungiyar adawa ta PDP su 27 kafin zaben gwamna a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, dan majalisar Kogi West ya yi wannan zargin ne a shafin yanar gizon a ranar Litinin, 11 ga Nuwamba.

9. Kogi: Natasha Akpoti ta tuhumi Yahaya Bello da kokarin kashe ta

A yayin da ake shirin zaben gwamna na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Natasha Akpoti ta zargi gwamna Yahaya Bello da aiko da wasu ‘yan ta’adda domin kona gidanta a Lokoja.

Akpoti ta shigar da karar ne a ranar Litinin, inda ta ce gwamna Bello ya tura ‘yan ta’adda a harabar gidanta a yayin da take gudanar da hidimar neman zabe a Idah.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Buhari: Matasan Arewa Sun Nemi Osinbajo da Ya Yaki Shugabancin Kasar Ko kuma ya yi Murabus da Matsayinsa

Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum ta tuhumi Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da mayar da harin tsanancin da fadar shugaban kasar ke yi masa.

Babban Shugaban Kungiyar Matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, a wata hira da jaridar Daily Post, ya lura cewa za a kori Osinbajo idan ya ki mayar da harin tsanantawa da wulakanci da ake masa, ko kuma ya yi murabus cikin mutunci da matsayinsa.

Shettima ya fadi hakan ne a yayin mayar da martani kan wasu sabin harin tsanantawa da kunyatarwa da mataimakin shugaban kasar ke fuskanta a fadar shugabancin kasa.

Shugana AYCF din ya nace a bayaninsa da cewa gwamnatin kasar a jagorancin Muhammadu Buhari tana tsanantawa Osinbajo, ya na kuwa mamakin abin da ya sa Mataimakin Shugaban kasar ya yi shuru game da rikicin da ke gudana da shi a Shugabancin.

“Mun gane da cewa wasu mutane a ofisoshin shugabancin kasar suna yin amfani da tsarin jagorancin ne don biyan bukatun kansu, Ko kun yarda ko kuma ku ki amincewa, akwai wani ko wasu da ke neman tabbatar da cewa an cire Mataimakin Shugaban kasa a tsarin mulkin don neman hanyarsa ta zuwa shugabancin kasar a 2023.” Inji Shettima.

“Abu daya nike bukatan ku gane a wannan gwamnatin, ko ta yaya suka ki amince da wannan zargin, tabbas akwai abin da ke gudana a boye. A daidai lokacin da suka ce Shugaban kasar da Mataimakinsa suna cikin kyakkyawan yanayi Na san wani abu da ba daidai ba na gudana, saboda ba a taba hayaki ba ba tare da wuta ba.”

“Maimakon a kori mataimakan Mataimakin Shugaban kasar, me zai hana a dubi Majalisar Dokoki ta kasa, idan da da gaske ake da son a rage kashe-kashen kudi a shugabanci a Najeriya me zai hana a nemi tsige wasu ma’aikata da ke a majalisar da basu da wata aiki na fari ko baka da suke yi, amma sai karban albashin da bai da ma’ana. Ko kuma a rage adadin yawar ‘yan majalisar, maimakon duba ofishin Mataimakin Shugaban.”

“Wasu daga cikin mu sun san cewa an zazzage fagen fama. Tabbas ana matukar raunana Osinbajo, wannan ya nuna a fili cewa ana hari da kuma neman a tsige shi ne daga tsarin mulkin. Na yi mamakin yadda bai fito ba da karfin gwiwa don neman tausayi da goyon bayan ‘yan Najeriya ya kuma bayyana zuciyarsa. Yana zaune kawai a cikin nutsuwa saboda yana son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shi mutumin Allah ne. Batun siyasa ba batun Allah bane, ya shafi batutuwa da yawa, tilas ne a nuna kwaraewa da iya taka rawa. Na san shi Farfesa ne na shari’a amma akwai bukatar ya fito ya fadawa ‘yan Najeriya abin da ke faruwa, idan ya ci gaba da yin shiru, kawai zai farka ne a wata safiya ya ga cewa an cire shi. “

Ka tuna a baya kamar yadda Naija News Hausa ta sanar, da cewa Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya yi zargin Shugaba Muhammadu Buhari da wulakantar da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a hanyoyi goma.