Connect with us

Uncategorized

Labari Mai Faranta Zuciya! Abubakar Daga Kiwo Yanzu Ya Zama Malami A Jami’ar Wukari

Published

on

at

Naija News Hausa ta ci karo da labarin wani mai suna Adamu Garba wanda labarin rayuwarsa ya zama abin farantar da zuciya da kuma abin koyi, musanman ga matasa.

Wannan kamfanin dilancin labarai ta samu fahimtar cewa Adamu Garba ya tashi ne daga kiwon dabbobi zuwa Mai Tsaro a Jami’ar ‘Federal University Wukari’, har zuwa zaman dalibin jami’ar.

Rahoton da Naija News Hausa ta gano a wata sanarwa ta tori.ng, sanarwar ta nuna da cewa Abubakar ya kammala karatunsa ne a jami’ar da sakamakon lambar yabo 2:1. A yanzu haka Malami ne tare da Sashen ilimin halayyar dan adam a wannan Makaranta.

An dauki Adamu Garba aiki ne a matsayin mai Tsaro da takardan kwaleji na NCE tun a ranar da shekarar 1/9/2012 akan CONTISS 5/2, ya yi auiki har ga tashi zuwa matsayi na CONTISS 8/2 a cikin wannan sashin. Bayan hakan ne ya Ya sami izinin shiga jami’ar don karshe karatunsa a jami’ar ta hanyar DE, kuma ya karshe karatun sa ne a farkon wannan shekarar. Yanzu haka shi Malami ne a Jami’ar.

Kalli Hoto a kasa;