Labaran Najeriya
Yadda El-Rufai Ya Nuna Mini Nasarar Buhari Tun Kafin Ma Zabe Ta Gabato – Femi Adesina
Femi Adesina, mai ba da shawara na musamman kan kafafen yada labarai ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana tattaunawar da ya yi da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gabanin babban zaben Najeriya.
Ya yi wannan wahayin ne a wata kasida mai taken ‘PMB a shekara ta 77:’ Don Allah ku fada wa Baba muna tare da shi har abada’, a yayin bikin tuna ranar haihuwar shugaban a ranar 17 ga Disamba.
Ku tuna da cewa Shugaba Buhari a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kayar da Atiku Abubakar na jam’iyyar Democratic Party (PDP) a zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2019.
Sakon Femi din na kamar haka:
“’Yan watanni kafin babban zaben shekarar 2019, na yi karo da Gwamna Nasir El-Rufai a fadar Shugaban Kasa, yayin da zai shiga don ganin Shugaban kasar. Mun gaishe da junanmu, sai kuwa na roke shi don Allah da tsayawa a ofishina a yayin kan dawowarsa daga ofishin shugaban kasar. Ya kuwa amince da yi alkawarin yin hakan.”
“Menene kuwa damuwa na? Sakonnin da nike cin karo da su a shafin sadarwa ta yanar gizo akan yadda zabukan za su gudana. Koda shike dai ina da zurfin sani game da gaskiyar, amma ina buƙatar dan tabbatarwa. Kuma na san El-Rufai shi ma nazarci ne, kuma yana da sani akan ƙididdiga a koyaushe.”
“Gwamnan kuwa ya bayyana. Na bayyana masa damuwa na, na nemi ra’ayin nasa. Kawai anan take ya bude kwamfyutar sa, ya kuwa bani dala-dalan sakamakon binciken kimiyya da yayi kan ra’ayin mutane ga sakamakon zaben.”
“Me binciken ya ce? Manyan sassan bincike daga ko’ina a fadin kasar, da kuma nazarin jihohi, ta bayyana cewa Shugaba Buhari zai kayar da abokin adawarsa da miliyoyin kuri’u.”
“Kari da cewa kafofin watsa labaru za su samar da zabuka tsakanin kashi tara zuwa 11 na kuri’un. Adadin kuwa ba zai zama ta jam’iyya daya kadai ba. Za a raba tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyun, da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma jam’iyyar Democratic Party (PDP). Wannan zancen kuwa ya tabbata kamar anabci.”
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Tsohon gwamnan jihar Anambra, Jim Nwobodo ya bayyana cewa bai dace ‘yan siyasa su fara fada kan yankin da ta dace da shugabancin Najeriya a shekarar 2023 tun yanzu.
Nwobodo, wanda ya mallaki kujerar gwamnan jihar Anambra a lokacin jamhuriya ta biyu, ya bukaci ‘yan siyasa da su kyale Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali kan mulkin kasar a yanzu.