Connect with us

Uncategorized

Shugaban Miyyeti Allah, Alhaji Kiruwa ya umurci ‘yan uwa da janye wa halin tashin hankali

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Alhaji Muhammed Kiruwa Ardon-Zuru ya umurci ‘yan uwar sa fulani da janye wa halin tashin hankali da farmaki akan zancen rama kashe-kashen da ake yi ga ‘yan uwar da ke a jihohi daban daban.

“Masu kashe-kashen al’ummar Fulani a yankunan kasar na hakan ne don tayar da hankali ga kasa da kuma neman raba hankalin mutane ne kawai” inji Alhaji Kiruwa.

“A matsayina na shugaba, ba na bukatar mutane na su mayar da farmaki, ko mayar da yaki ga mutanen da suka kashe ‘yan uwar su”

“Na gane da cewa masu kashe-kashe ‘yan uwarmu Fulani a Jihar Kaduna, Taraba da Jihar Benue su na hakan ne don tada tanzoma a kasa” inji fadin Alhaji Kiruwa a bayanin sa da manema labarai a Birnin-Kebbi.

Alhaji Kiruwa ya kuma bukaci hukumomin tsaro da cewa su yi kokarin anshe makamai da kuma daukar mataki ta musanman ga wadanda ke aiwatar da irin wannan halaye a Jihohin da kashe-kashen ya shafa.

Ya karshe da cewa, “Kungiyar mu zata hada kai da hukumomin tsaron kasar duka don magance irin wannan shiri na tashin hankali a kasa”.

Karanta wannan kuma: Iyalin mutane shida 6 sun kone kurmus da wuta a Jihar Kano