Connect with us

Uncategorized

Jihar Benue ta rasa mutane 16 a wata harin Makiyaya a ranar Lahadi da ta gabata

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jihar Benue a ranar Lahadi 3 ga watan Maris, 2019 da ta gabata ta fuskanci wata sabuwar mumunar hari daga hannun makiyaya a kauyan Tse-Kuma, yankin Mbachohon ta karamar hukumar Gwer ta Yammacin Jihar.

A killa mutane goma sha shidda suka rasa rayukan su, kamar yadda aka bayar ga manema labarai daga bakin Ciyaman na karamar Hukumar Gwer, Mista Francis Ayaga.

“Makiyayan sun hari yankin ne a ranar Lahadi da harbe harbe” inji mista Francis. Ko da shike Kwamandan Operation Whirl Stroke ( OPWS), Meja Janar Adeyemi Yekini, ya bayyana da cewa hukumarsu ta samu gano gawakin mutane bakwai (7) ne kawai a lokacin da aka karbi wannan rahoton.

“Sun fado wa yankin mu ne da shanaye da yawa cikin gonaki da cin hatsin mutane da kuma barnan kayakin gona duka. A bayan haka suka fada wa manoman da harbi har suka kashe kimanin mutane goma sha shidda” inji fadin Francis Ugbede, mazaunin yankin a bayanin sa da manema labarai.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga sun kashe mutane 16 a Jihar Benue