Connect with us

Uncategorized

PDP sun yi karar Alkali Inyang akan hana gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) sun gabatar da karar Alkalin da ya hana hukumar gudanar da hidimar zaben Jihar Bauchi daga sanar da sakamakon zaben tseren kujerar Gwamnoni da aka yi a Jihar ‘yan kwanaki da suka gabata.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun Koli ta Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya, a jagorancin Alkali Ekwo Inyang ta umurci hukumar INEC da dakatar da hidimar gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi.

Jam’iyyar PDP sun bayyana matakin a matsayin rashin bin dokar zaben kasa ga Alkali Inyang. “Wannan matakin ta karya dokan zabe da kuma dokar kasa” inji PDP.

Sun dage da cewa Inyang ya take da kara dokar zaben kasa kamar yadda take a cikin shafi na 87(11) ga dokar zaben kasa wanda ya bayar da cewa “Babu kotun da ta isa ta dakatar da hidimar zaben da ba a kamala ba”

Jam’iyyar PDP sun gabatar ne da hakan a bayyanin da aka bayar daga bakin Ciyaman na Jam’iyyar PDP ta Tarayyar Kasa, Prince Uche Secondus, a nan birnin Abuja ranar Talata da ta gabata.

“Duk da cewa doka ta bayyana matakai da sharidu ga hidimar zaben kasa, alkali Inyang bai bi hakan ba sai dai ya karya dokar” inji shi.

Uche ya bukaci babban Alkalin kasar (NJC) da daukar matakin da ya kamata akan karar, da kuma taimaka da ribato yancin dimokradiyyar kasar Najeriya.