Uncategorized
AAC sun dakatar da Ciyaman na Jam’iyyar su, Sowore
Jam’iyyar Siyasa ta African Action Congress (AAC) sun gabatar da dakatar da Omoyele Sowore a matsayin Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar, hade da wasu kuma daga Jam’iyyar.
Naija News ta gane da hakan ne a wata sanarwa da Ciyaman na Kwamitin Jam’iyyar ya bayar a yau Litini, 13 ga watan Mayu, 2019 a birnin Abuja.
Ka tuna da cewa Omoyele Sowore na daya daga cikin ‘yan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya daga Jam’iyyar AAC, a zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka kamala a baya.
Bisa ganewar wannan gidan labarai tamu, Jam’iyyar sun dakatar ne da Sowore akan laifin kadamar da Makirci, halin cin hanci da rashawa, da kuma rashin bayyana ga wata zama da Jam’iyyar ta yi.
Kwamitin Jam’iyyar (NEC) sun nada Mista Leonard Nzenwa a matsayin sabon ciyaman na Jam’iyyar bayan da aka dakatar da Sowore.
Naija News Hausa ta kuma gane da cewa ba Sowore ne kawai Jam’iyyar suka dakatar ba, amma har da rukunin shugabancin sa a Jam’iyyar.
KARANTA WANNAN KUMA; An Kashe wani Jigon Jam’iyyar APC a Jihar Rivers