Connect with us

Labaran Najeriya

Majalisa ta gabatar da zancen mayar da ranar 12 ga Watan Yuni sabon ranar Dimokradiyyar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Alhamis da ta wuce, Majalisar Dattijai sun gabatar da sabon bil na komar da ranar 12 ga watan Yuni ta kowace shekarar a matsayin ranar Dimokradiyya.

Hakan ya biyo ne bayan da Ahmad Lawan, jagoran zaman Majalisar ya gabatar da bil din a gaban gidan Majalisar a ranar Alhamis.

Ko da shike Naija News na da sanin cewa an riga an gabatar da zance a zaman gidan Majalisar tun watan Disamba ta shekarar 2018 da ta gabata.

Ka tuna a baya kuma cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da cewa za a musanya ranar 29 ga watan Mayu da ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar tunawa da komawar Gwamnatin farar hula.

Shugaba Buhari ya gabatar da hakan ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta tuna da nasarar Moshood Abiola, ga zaben shekarar 1993.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan Majalisar Dattijai da Majalisar Dokokin Tarayyar Kasar Najeriya bisa shugabancin kasar.

Buhari ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin shugabancin kasar da majalisar dokoki ta 8 da suka gama shugabanci ba ta zama da kyau ba, kuma kasar ta cancanta da dangantaka fiye da hakan.

Ya ce, “hulɗar tsakanin manyan hukumomar kasar da majalisar dokoki bai kasance mafi kyau ba a majalisar dokoki na 8”

“Ina fatan kowa da kowa zaiyi iya kokarinsa don tabbatar da kyakkyawan dangantaka tsakanin bangarorin biyun a Majalisar Dinkin Duniya ta 9 da zata dauki shugabanci, domin mu iya taimaka wa al’ummar kasa a hanya mafi kyau,” inji Buhari.