Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 29 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 29 ga Watan Mayu, 2019

1. Ranar Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a karo ta biyu

A yau Laraba, 29 ga watan Mayu, za a gudanar da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a Ofishin shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu, na tsawon shekaru hudu kuma.

Wannan hidimar rantsarwa tabbaci ne ga nasarar Buhari a zaben shugaban kasa ta watan Fabrairu da ya gabata, a karkashin Jam’iyyar APC.

2. Za a rantsar da Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya a yau

Yau ne za a gudanar da hidimar rantsar da wasu Gwamnoni a kujerar jagorancin Jihohi a Najeriya bisa sanarwan da aka bayar a baya da ya bayyana ranar 29 ga Mayu, a matsayin ranar rantsar da shugabannai a kasar.

Wannan tabbaci ne ga nasarar da gwamnonin suka yi ga zaben 2019 da aka kamala a baya, a jagorancin hukumar INEC.

3. Wani Ma’aikaci ga Gwamnan Jihar Borno ya dauke ransa

Mista John Achagwa, wani babban ma’aikaci ga gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, ya kashe kansa a gidan gwamnatin Jihar Borno da ke a Maiduguri.

Naija News Hausa ta samu fahimta da cewa Mista John ya rataya kansa ne da igiya a bayan gidan hutun shugaban kasa da ke a Maiduguri, a ranar Talata da ta wuce.

4. Kwamitin Sarautan Kano ta bada umarnin kame ma’aikaci ga Sarkin Kano, Sanusi

Kotun Majistire da ke a birnin Kano, a ranar Talata da ta gabata ta bada umarnin a kame mutane Uku hade da Mannir Sanusi, babban ma’aikacin tsaro ga Muhammadu Sanusi II (Sarkin Kano).

A fahimtar Naija News Hausa, Kotun tayi hakan ne bisa wata zargin cin hanci da rashawa da kuma makirci da aka gane su da ita na kudi naira Biliyan Hudu.

5. ‘Yan Hari da Makami sun kashe kimanin mutane 23 a Zamfara

A ranar Talata da ta wuce, Mahara da bindiga sun kai sabin hari a kauyan Kabaje da Tunga da ke a karamar hukumar Kauran Namoda, ta Jihar Zamfara.

Harin ya faru ne a missalin karfe biyar na safiyar ranar Talata da ta wuce.

6. An daga karar Cin Hancin da ake ga tsohon Gwamnan Jihar Katsina

Alkali Hadiza Shagari da ke wakilci a Kotun Koli ta Jihar Katsina, a ranar Talata da ta wuce ta daga karar Ibrahim Shema, tsohon Gwamnan Jihar Katsina zuwa ranar 26 ga Yuni ta shekarar 2019.

Naija News ta fahimta cewa Alkalin ta gabatar da hakan ne bisa rashin kasancewa mai daukan kara daga Hukumar EFCC da kuma wakili daga gwamnatin Jihar, a gaban kotu.

7. Ruduwa a rukunin Jam’iyyar APC a yayin da aka bukaci Oshiomhole da janye kansa daga jagoraci

Mataikin Ciyaman na Jam’iyyar APC ta Tarayya ga hidimar neman zabe ga Jam’iyyar, Lawali Shuaibu, ya gabatar da bukatar cewa Adams Oshiomhole, Ciyaman na Jam’iyyar ya janye daga zaman sa a matsayin Ciyaman na Jam’iyyar.

Wannan ya biyo ne bayan da Kotu ta gabatar da dan takaran Jam’iyyar PDP ga zaman mai nasara ga hidimar zaben kujerar Gwamnan Jihar Zamfara.

8. 2023: Afenifere ta mayar da martani ga zance Tinubu da neman zama shugaban kasar Najeriya a gaba

Hadaddiyar Kungiyar Yarbawar Najeriya ‘Afenifere’ sun mayar da martani game da zancen cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu na kokarin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Kungiyar sun bayyana cewa an shiga rudun mutanen Najeriya a layin yanar gizo da zancen cewa Tinubu na da kudurin maye gurbin Buhar a shekarar 2023.

9. Dalilin da ya sa na ji tausayin Oshiomhole – Fani-Kayode
Tsohon Ministan Harkokin Jirgin Sama, Femi Fani-Kayode ya bayyana da cewa Jam’iyyar APC sun yi amfani da Oshiomhole kamar ragga, suka kuma yi watsi da shi.

Ka tuna a baya, Lawani Shuiab, mataimaki ga ciyaman na Jam’iyyar APC na Tarayya ya bukaci Adams Oshiomhole da janye daga kujerar ciyaman na Jam’iyyar APC.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com