Uncategorized
Yan sanda sun karbi kudi daga yan yankin Nasarawa don magance matsalar Makiyaya – Amnesty International
Yan Sanda su karbi kimanin kudi dubu dari da hamsin daga yankin Nasarawa don magance matsalar makiyaya a yankin
Wasu mazauna Jihar Nasarawa sun shaidawa Amnesty International (AI) da cewa ‘yan sanda da aka aika a yankin don magance matsalar makiyaya sun bukace su da biyar kudi mai kimanin naira Dubu dari da hamsin (N150,000).
Mazauna bayyana wannan zargin ne ga wata rahoto da AI ta bayar game da rikici tsakanin manoma da makiyaya a kasar.
Rahoton na kamar haka: “Wasu mazauna yankin Nasarawa da yankin Kokona da kuma Agwada, Udege, da kuma yankin Loko, a ranar 10 ga watan Maris na 2017 sun rubuta takarda zuwa ga Babban Jami’in Sojan Sama na neman taimako bisa irin mugun hali da suke ciki da Fulani makiyaya a yankin.
“Sojoji sun rubuta wasika zuwa ga Babban Shugaban Yan Sanda (IGP), ya sanya takardan da rokon IGP su da nuna kulawa da wannan al’amarin kuma ya dauki mataki mai dacewa”.
“Hukumar ta IGP ta tura wasikar zuwa ga Mataimakin Janar na ‘yan sanda da ke kula da Harkokin ta’addancin”.
“Yan kauyukan sun gayawa Amnesty International cewa Yan sanda da aka turo don magance matsalar rikici a yankin sun bukace su da biyan kudi mai kimanin naira Dubu dari da hamsin (N150,000) don bukatu. kuma sun biya wannan kudi”.
Yan Sanda sun hallara a ofishin yan sanda dake a kauyen Agwada a ranar 25 zuwa 27 a watan Biyar, 2017, inda suka bukaci wasu mutane daga kauyen don su zo su bada tabbacin wannan magana.
“Fadin wani mazaunin kauyen, yace Yan Sanda sun ki su shiga kauyen, da fadin cewa kauyen ba ta da hanyar bi mai kyau, kuma yan ta’addan Fulanin na da makamai masu karfi da kyau bisa na yan sanda.
Isa Sanusi, Kakanin yawun AI, ya bayyana zargin yan kauyen ne ga layin yada labarai a ranar Talata.
“Ina iya tabbatar maku da wannan. akwai shaidu, komai da aka fada a rahoton gaskiya ne an sa su biyan kudi,” in ji Shi.
Kakakin yawun Yan Sanda, Jimoh Moshood ya ce ya tuntubi masu bincike ta’addanci a ofishin amma Ofisan ya yi musu da wannan cewa ba bu wanda ya tambayi mazauna yankin kudi.
“Karya ne, na binciki wannan bayyan karban sakon da aka aika mani kuma in tabbatas maka da cewa duk karya ce. babu dan sanda da zai bukaci kudi daga al’umma, Ya gaya wa manema labarai.
Naija News ta ruwaito Yan siyasa su guje wa halayen da za su iya haifar da tashin hankali – in IGP