Connect with us

Uncategorized

‘Yan Fashi sun kashe Mutane Bakwai a sabuwar hari a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Fashi sun kashe mutane bakwai da sace mutane shidda (6) a kauyuka 10 da ke a karamar hukumar Kankara, a Jihar Katsina ranar Asabar da ta gabata.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hakan ya faru ne a karshen makon da ta gabata a kauyukan, Pawwa, Katoge, Korawa, Dan Hayi, Gidan Mai Godiya, Gidan Dan Maarbi, da Yar Kuka.

Rahotannai sun sanar da cewa ‘yan fashin sun kone Gidaje da Shaguna a harin da aka kai kauyukan misalin karfe 5 na maraice zuwa karfe 7. A bayanin da manema labarai suka bayar, a sanar da cewa Mata Uku hade da Yara Uku ne aka sace a harin.

Ganin hakan, Matasan kauyan Irate suka fita da maye hanyoyin yankin da zanga-zanga, harma da hanna matafiya daga Sokoto, Kano, da Katsina bin hanyar garin.

An bayyana da cewa masu zanga-zangar sun haura da gawakin mutanen da aka kashe zuwa fadar sarkin garin Kankara. Inda suka zargi hukumomin tsaro da rashin kadamar da ayukansu yadda ya dace.

“Akwai katangewar bincike na Jami’an Tsaro goma tsakanin Yantumaki da Kankara, amma abin takaici, kullum mahara da ‘yan fashi ke kawo hari da kadamar da ayukansu a yankin, kuma hukumomin tsaron su kasa daukan mataki ga hakan” inji zargin da wani mazauna yayi ga Jami’an tsaro.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan Fashi 29 a Zamfara.

Rukunin Sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji sun kai harin wutan ne ga ‘yan fashi da ke a gandun dajin Moriki na Jihar Zamfara, inda suka ci nasara da kase 29 daga cikinsu.