Connect with us

Uncategorized

Boko Haram Sun hari Motar Gwamnan Borno a Konduga

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan ta’addar Boko Haram a daren ranar Alhamis da ta gabata, sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, a yayin da yake kan wata ziyarar aiki.

Naija News ta fahimci cewa ‘yan ta’addan sun hari ayarin gwamnan ne da ke a Konduga yayin da shi da tawagarsa suke dawowa daga tafiya zuwa karamar hukumar Bama.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, abin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare ranar Alhamis din bayan Zulum ya ziyarci Bayo, Kwaya Kusar, Askira Uba da Gwoza a shirin sa na zagayen kananan hukumomin Jihar guda 27.

Ko da shike, an bayyana da cewa Gwamna Zulum da duk wadanda ke cikin motocin sun sami tsira daga lamarin ba tare da wata rauni ba.

“Abin mamaki gwamnan da Kwamishanoni hade da sauran mutane da ke a cikin motocin sun tsira daga harin, amma dai abin takaici sun lallata motar da ke dauke da sojojin da ke biye da Gwamnan da arsasun bindia ko ta ina.”