Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 6 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 6 ga Watan Satunba, 2019

1. Sanusi, Fayemi, El-Rufai sun yi Liyafa a South Afirka a yayin da ake Kashe ‘yan Najeriya a kasar

An gano mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a yayin da yake Liyafa a kasar South Afirka tare da Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, Gwamnan Jihar Ekiti da Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna a yayin da ake kisa da tsananta wa ‘yan Najeriya a kasar.

Wannan ya bayyana ne a lokacin da ‘yan Najeriya suka daga murya game da bayyanar Jim Ovia da sauran’ yan Najeriya, har da tsohuwar minista Oby Ezekwesili a taron tattalin arzikin duniya na Afirka 2019, wanda ke gudana a Cape Town, kasar South Afirka.

2. Kotu ta Tsige memba na APC a majalisar wakilai, ta kuma umarci PDP ta karbe ragamar mulki

Kotun daukaka karar Majalisar Dattawa da ke zaune a Calabar, a ranar Laraba da ta wuce ta tsige Mista Alex Egbonna na Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai wakiltar mazabar tarayyar Abi da Yakurr a Jihar Cross River.

A hakan ne Kotun ta yanke hukuncin bada damar maye gurbin ga dan takarar kujerar daga Jam’iyyar PDP, Mista John Gaul Lebo.

3. Rikicin Tiv da Jukun: CAN ta yi kirar sassauci

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga kabilun Jukun da Tiv da ke fada a jihohin Taraba da Benue da su rungumi zaman lafiya.

Wannan rokon ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja ta hannun Shugaban Kungiyar ta CAN, Mai Martaba, Rev Dr Samson Ayokunle.

4. Gwamnatin Tarayya ta Bayyana Dalilin da ya sa Fayemi, El-Rufai da Sarki Sanusi suka ziyarci kasar South Afirka

Gwamnatin Tarayya ta kare gaban Gwamnonin Najeriya, Nasir El-Rufai, Kayode Fayemi da Sarki Lamido Sanusi a kasar South Afirka.

Wannan ya biyo ne bayan kalubalantar da ‘yan Najeriya suka yi bisa hotunan shugabannin Najeriyar da aka gano a yayin da suke liyafa a taron tattalin arzikin duniya na Afirka 2019, wanda ke gudana a Cape Town, South Afirka.

5. Xenophobia: Yawancin Bidiyon da aka fitar game da Hare-hare a South Afirka ba gaskiya ba Ne – Lai Mohammed

An shawarci ‘yan Najeriya da su daina yada faifan bidiyon karya da ake yadawa kan hari da ‘yan kasar South Afirka ke kai wa ‘yan Najeriya a can.

Lai Mohammed, ministan labarai da al’adu ne ya ba da shawarar yayin da ya ce wasu mutane suna amfani da wadannan labarai / bidiyo na karya don haifar da matsala a kasar.

6. Dino Melaye ya ki amince da Sakamakon zaben Firamaren Gwamnonin PDP a Jihar Kogi

Sanata mai wakiltar Yammacin Jihar Kogi a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Dino Melaye, ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani a zaben Firamare ta jam’iyyar PDP a Jihar.

Naija News Hausa ta tuna da cewa ba da dadewa ba Kotun sauraren kararrakin zaben majalisar dattijai da majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da Sanata Melaye, wanda ya tsaya takara tare da sauran yan takarar.

7. Ministan Harkokin Wajen South Afirka ya bayyana sanadiyar ikanin Dalilin ‘Yan Najeriyar, Ana Cin Zalincin Kasashen waje

Ministan Harkokin Wajen South Afirka, Naledi Pandor, ya fada da cewa wariyar launin fata ga wasu kasashen Afirka ne sanadiyar matsalolin da ke haifar da mumunar hare-hare a kasar.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da aka tilastawa wa Pretoria da rufe ofishin jakadancinta a Najeriya saboda tsoron hare-haren daukar fansa.

8. Xenophobia: Babban Minista Kadamarwa ta South Afirka ta kulle Ofishinta a Najeriya

Sakamakon tashin hankali da harin da ‘yan Najeriya ke kai wa kasuwanci da Mallakar kasar South Afirka a Najeriya, an rufe ofishin jakadancin South Afirka a Najeriya har sai an samu ci gaba da sanarwar hakan.

Babban Kwamishina, Amb. Bobby Moroe, wanda ya tabbatar da rufewar ya ce ya umarci Ofishin Jakadancin da dakatar da dukkan ayyukan ofishin jakadancin har sai an samu sassauci ga lamarin.

Karanta kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa