Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 9 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 9 ga Watan Satunba, 2019
1. Buhari Zai Ziyarci Shugaban South Africa, Ramaphosa
Fadar Shugabancin kasa ta dage da cewa ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar South Afirka don ganawa da Cyril Ramaphosa, shugaban kasar kan sabbin hare-hare da ake yi ga ‘yan Najeriya a kasar ya zan dole.
Naija News ta fahimta da cewa Shugabancin kasar ta fadi hakan ne a wata sanarwa a ranar Asabar.
2. Edo: Oshiomhole yayi Magana kan Riciki tsakanin sa da Obaseki
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa takaddamar da yayi da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ba wani sirri bane.
Da yake bayani da gidan talabijin na Channels TV a ranar Asabar, Oshiomhole ya ce sassaucin ba batun kudi bane ko alƙawura.
3. Masu Zanga-zangar Sun Nemi ‘Yan Kasashen waje da Su bar kasar South Afirka
Masu zanga-zangar dauke da makamai a kasar South Afirka a yanzu sun yi barazana da bin titunan kasar don nuna adawarsu da cewa baki daga kasashen waje su koma inda suka fito.
Wata jaridar kasar South Afirka Sowetan Live ta bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar, wadanda ke dauke da makamai suna jirar bayani ne daga Mangosuthu Buthelezi, wani fitaccen dan siyasa kuma shugaban kabilan Zulu kamin su ci gaba da kudurin su.
4. Ministocin Abuja FCT sun aika da gargadi ga Yan siyasa, jam’iyyun gabaci zaben Kogi
Ministan birnin Tarayya (FCT), Dokta Ramatu Tijjani Aliyu, ta gargadi ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da su kula da kalamansu kafin zaben gwamna na Kogi.
Naija News ta gane da cewa cewa Ministan ya sanar da hakan ne lokacin da yake karbar mambobin majalisar dokokin jihar Kogi.
5. Wakilan Musamman sun Komo Ga Shugaba Buhari da bayanai
Wakilai ta musamman da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya aika zuwa kasar South Afirka bayan harin ta’addancin da aka yi wa ‘yan Najeriya, sun dawo kasar.
Wakilin na musamman wanda har ila yau shi ne Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA), Ahmed Abubakar, ya dawo kasar bayan da ya gana da Shugaba Cyril Ramophosa na kasar South Afirka.
6. IMN: ‘Yan Shi’a sun gabatar da ranar Hidimar su duk da dokar Hana Hidima da Kotu ta bayar
Duk da sammaci da Kotun Najeriya ta gabatar, Kungiyar Ci gaban Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wacce kuma ake wa lakabi da Shi’a, ta tsayar da ranar Talata don bikinta na Ashura.
Naija News ta fahimci cewa hidimar Ashura wanda kuma ake kira da ranar Ashura, rana ce ta goma ga Muharram, watan farko a kalandar Musulunci.
7. Abin da PDP ta ce game da yin Watsi da Gwamna Makinde
Jam’iyyar PDP, reshen jihar Oyo ta yi watsi da jita-jitar cewa shugabanta ya tumbuke Gwamna Seyi Makinde.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran Jam’iyyar, Akeem Olatunji ya bayar, PDP ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da nuna halin kokarin murkushe Makinde.
8. Zaben Kogi: Gwamna Yahaya Bello ya zabi sabon mataimakin ga Takara
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ba gabatar da cewa ya zabi Chief of Staff, Edward Onoja, a matsayin abokin takarar sa a zaben gwamna mai zuwa.
Naija News na da sanin cewa an sanar da yin zaben gwamnan a Jihar Kogi ne a ranar 16 ga Nuwamba.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shagin Hausa.NaijaNews.Com