Connect with us

Labaran Najeriya

Sama da ‘Yan Najeriya Miliyan 40 basu da aikin yi, Miliyan 90 kuma cikin matsanancin Talauci – Ministan Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hajia Sadiya Umar Farouq, Ministan Bayar da Agaji na Najeriya, Gudanar da Habaka Bala’i da Ci gaban Al’umma, ta bayyana cewa a yanzu haka sama da ‘yan Najeriya miliyan 40 ba su da aikin yi.

Sadiya ta ba da sanarwar mai damuwa ne lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin majalisar game da al’amuran mata da ci gaban zamantakewa don kare kasafin kudin ma’aikatar na shekarar 2020.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya ranar 11 ga watan Oktoba 2019, da gano wasu hotuna da bidiyo iri-iri akan layin yanar gizo wanda ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari na shirin aure da Sadiya Umar Farouq, Ministan Harkokin Agaji ga kasar Najeriya.

Ko da shike da baya gaskiya ya bayyana da cewa zancen ba gaskiya bace.

KARANANTA WANNAN: Kiwon Lafiya: Amfanonin Ganyan Zogale a Rayuwar Dan Adam.