Uncategorized
APC/PDP: Kalli Cikakken Sakamakon Zaben Sanata a Jihar Kogi
Hukumar Zaben Kasa (INEC) ta Gaza Tabbatar da Mai Nasara ga Zaben Sanata a Jihar Kogi
Naija News Hausa ta ruwaito da zaben tseren neman kujerar gidan majalisar dattijai wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2019 a Jihar Kogi, wanda ya kunshi ‘yan takara ashirin da hudu (24) hadi da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dino Melaye da Smart Adeyemi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wadanda suka kasance manyan ‘yan adawa a takarar.
A yayin da ake sanar da sakamakon zaben a daren Lahadin da ta gabata, babban jami’in hukumar INEC wanda ke tattara sakamakon zaben, Olayinde Lawal, ya bayyana da cewa yawar kuri’u da aka tsoke ya fiye kuri’un da ke tsakanin manyan ‘yan takarar biyu daga Jam’iyyar PDP da APC.
Lawal ya ce yayin da Adeyemi ya samu yawar kuri’u 80,118, shi kuma Dino Melaye ya samu kuri’u 59,548, wanda ya nuna banbancin kuri’u 20,570.
Da cewa yawar kuri’u da aka soke itace 43,127 a cikin kananan hukumomi bakwai na inda aka gudanar da zaben.
Duba sakamakon a kasa:
Kabba/Bunu LGA
APC-15,037
PDP-8,974
Ijumu LGA
APC-11,627
PDP-7,647
Kogi/Koton Karfe LGA
APC-14,168
PDP-9,786
Mapo/Muro LGA
APC-4,874
PDP-3,704
Yagba East LGA
APC-6,683
PDP-7,745
Yagba West LGA
APC-7,941
PDP-8,980
Lokoja LGA
APC-19,788
PDP-12,712