Uncategorized
Kalli Wadanda Aka Bayyana Da Bada Goyon Baya ga Boko Haram
Fani-Kayode ya Tona Asirin Masu Tallafawa Boko Haram
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya zargi kungiyar ISIS, AL-Qaeda, Saudi Arabiya, Qatar da kasar Turkey da tallafawa kungiyar Boko Haram a Najeriya.
Bisa fahimtar Naija News a cewar wani rahoto da aka bayar a gidan talabijin labarai ta News Channel, an bada tabbacin cewa kasar Turkey ta kasance babbar mai bada makamai ga kungiyar Boko Haram.
A yayin mayar da martani kan zancen, hedikwatar tsaron kasar ta ce matakin rufe Iyaka Najeriya, hadi da wasu matakai zai taimaka wajen shawo kan makamai da ake shigarwa a kasar da ba bisa ka’ida ba.
“Kodayake babu cikakkiyar tabbaci tukuna kan ikirarin da aka yi a faifan bidiyo din cewa kasar Turkey ce ke tallafawa ‘yan ta’addar Boko Haram da makama, Amma dai wannan lamari ne mai mahimmanci kan tsaron ƙasar, amma kuma akwai tabbacin cewa a haka ana daukar matakai don shawo kan lamarin.” inji bayani daga Hedikwatar tsaron kasar.
Fani Kayode a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @realFFK, ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta nemi taimakon Shugaban Amurka (Amurka), Donald Trump da Isra’ila don shawo kan masu tayar da kayar baya.
“Kasar Turkey, Qatar da Saudi Arabiya suna ba da goyon baya ga kungiyar Boko Haram da kuma rikicin Fulani makiyaya. ISIS, Al Qaeda da Jihadin Islama suna yin hakan a bayyane.”
“Abin da ke faruwa a hankali a cikin kasarmu na da matukar ban tsoro kwarai da gaske. Najeriya na bukatar goyon bayan Donald Trump da Isra’ila kan abin da ke a gaba” inji Fani Kayode.