Connect with us

Uncategorized

Majalisar Zartarwar Zamfara ta Soke Dokar Bayar Da Fansho Ga Tsoffin Gwamnonin, Da Wasu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta soke dokar da ta amince da biyan fansho da wasu hakkoki ga tsoffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da sauran masu rike da mukaman siyasa a jihar.

An gabatar da wannan matakin ne a ranar Talata da ta wuce a yayin zartawa da Majalisar jihar ta yi gidan majalisar dokoki a Gusau, babban birnin jihar.

Jagoran majalisar, Faruk Dosara (PDP Maradun I), wanda ya gabatar da kudirin, ya gargadi sauran ‘yan majalisar da su yi la’akari da dokar.

Ya ce dokar ta wuce gona da iri ga tsoffin shugabannin siyasa na jihohi, a yayin da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya na a zube ba tare da biya su hakkinsu ba da tsawon shekaru.

A cewarsa, wannan rukunin shuwagabannin da suka gabata suna karbar sama da naira miliyan N700 a duk shekara, ya fada da cewa a wannan lokacin da tattalin arzikin jihar ta raunana, jihar ba zata iya cinma biyan irin wannan ba.

Tukur Tudu (PDP Bakura), yayin da yake gabatar da kudirin a karo na biyu, ya yi bayanin cewa rusa dokar ta zama mai matukar mahimmanci kamar yadda hakan ke cutarwa ga tattalin arzikin jama’a.

Bayan tattaunawa da kuma gudummawa da mambobi suka bayar, Shugaban majalisar, Nasiru Magarya, ya umarci Magatakardan majalissar da ya gabatar da kudirin a karatun farko da na biyu.

A cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a ranar Talata, Majalisar Jihar Zamfara ta bayyana da cewa duk shugabannin siyasa da suka shude a jihar ba za su sake samun wani cancanci ba kamar yadda aka saba, musanman karban manyan kudade da biyan wasu bukatu.

KARANTA WANNAN KUMA; Kotu Ta Gurfanar Da Alhaji Ibrahim Danmaliki kan Zargin Batanci.