Connect with us

Uncategorized

Jami’ar FUTA ta kori Dalibai shida da suka Ci Mutuncin Wata Daliba (Kalli Bidiyon a Kasa)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’ar Federal University Of Technology Akure (FUTA) ta kori wasu dalibanta shida sakamakon cin zarafin wata daliba.

Naija News ta tunatar da cewa daliban da aka kora sun fada cikin daya daga dakunan daliban jami’ar inda suka hari wata yarinya da bugu, suka yi awon gaba da ita tare da cire kaya, suka mayar da ita tsirara harma da yin rikodin abin da ya faru da wayoyi.

An tattaro cewa daliban sun azabtar da ‘yar uwarsu daliban har ga bakin mutuwa wai don ta kira ‘yan matan karuwai.

A cewar Mataimakin Darakta, Kamfanin Sadarwa na Cibiyar, Adegbenro Adebanjo, ya ce korar da aka yiwa daliban ya biyo baya ne bisa ga shawarar kwamitin bincike wanda suka bayar da labarin abin da ya faru a cikin harabar makarantar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2019.

Ga sunan Daliban da aka kora kamar haka:

1- Popoola Olaniyi Agboola IDD / (300L)

2- Oluwadare Faith Tobiloba FST (200L)

3- Nandi Yohanna Jessica IPE / (200L)

4- Ajuwon Tolani Emmanuella FAT / (100L)

5- Emmanuel Funmilayo Taiwo FAT / (100L) da kuma

6- Alao Olabimpe Cecilia CSP / (100 L)

Kalli Bidiyon Yadda Aka Azabtar da Yarinyar a Kasa;

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da rahoton yadda aka kori wasu ‘yan madigo hudu a makarantar Jami’ar Kebbi state College of Science and Technology. 

Bisa bayanin Babban Malami da kuma mai jagorancin Makarantan Jami’ar da a Turance ake kira ‘Povost’, Mista Aminu Dakingari ya bayyana da cewa masu tsaron makarantar, tare da masu tsabtace makarantar ne suka gane da ‘yan matan a lokacin da suke kokarin yin madigo da junar su a dakin barcin dalibai.