Uncategorized
Taya Smart Adeyemi Murnar Nasarar Zabe, Kamar Taya Barawo Murnan Sata Ne – Dino
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, a mazabar Kogi West Senatorial a zaben cika tsere da aka kamala a jihar Kogi, Dino Melaye, ya bayar da dalilan da suka sa ba zai taya Smart Adeyemi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) murna ba.
Ka tuna da cewa Naija News ta ruwaito da cewa Olayinde Lawal, jami’in kula da gudanar da hidimar zaben na ranar Asabar ya bayyana Smart Adeyemi na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben jihar.
Sakamakon zaben ya bayyana Dan takarar jam’iyyar APC da samun kuri’u 88,373 inda ya kayar da Dino Melaye na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), abokin hamayyarsa na kusa, mai yawar kuri’u 62,133.
Amma, shi Melaye a shafinsa na Twitter a ranar Lahadin da ta wuce ya ce,
“Taya Smart Adeyemi murna da nasarar zaben a gani na kamar ka taya dan fashi murna ne bayan nasarar da ya samu daga kwace” inji SDM.
“Godiya ta na musanman ga Allah madaukakin sarki da ya ceci rayuwata bayan yunkurin kisan kai 5, hada hadadden hukumomin tsaro, INEC, tarayya, jihohi da ikon karamar hukuma. An yi ya?i da ni a ?asa, a kan iska da kuma ruhaniya. Ba batun zabe bane illa rayuwata. Allah, na gode.”
“Zan kalubalanci nasarar Adeyemi na dan lokaci. Nasara ta hanyar tashin hankali da yaudara alama ce ta faduwa, domin wannan zaben an saye ta ne. Ba batun Dino MELAYE bane, wannan ya shafi Najeriya ne da tsarin zaben mu. Na ci gaba da ayuka na, bata kare a nan ba.”
“Halin maza da mata kan fatan alheri a duk fa?in Najeriya musamman kyawawan mutanen Kogi yamma wa?anda suka za?a ni, da gaske shaida ce da cewa Allah na tare da ni, kuma tare da mu duka. Na ci zaben” inji Dino.