Connect with us

Uncategorized

Sarkin Bauchi, Dakta Adamu Ya Gargadi Uwaye Masu Sanya Yaransu Auren Dole – Karanta Bayaninsa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mai martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Adamu, ya gargadi iyaye game da tura da tilasta wa ‘yan mata masu kananan shekaru cikin aure.

Sarkin Ya bayar da hujjar cewa, irin wannan dabi’ar, na kawo babban hatsari ga kananan ‘yan matan da ake aurarwa.

Ya ba da gargadin ne yayin bikin saukar karatun ‘yan mata 448 da suka kamala horar su a kwarewar rayuwa wadda kungiyar reshen jihar Bauchi ta Tarayyar Matan Musulmai a Najeriya da kuma Gild is Gold Foundation ta shirya, wanda aka gudanar a Kwalejin Gwamnatin Mata a Bauchi.

Adamu ya kuma shawarci iyaye da su daina sanya kananan ‘yan mata a harkar talla a kan tituna da boyewa a karkashin yanayin bunkasa tattalin arzikinsu.

Ya jaddada cewa irin wadannan ayyukan suna lalata tarbiyyantar da ‘yan mata a cikin al’umma.

Sarkin, wanda Dan-Isan Bauchi, Alhaji Ibrahim Yakubu III ya wakilta, ya kuma yi kira ga iyaye da su yiwa yaransu rajista, musamman kananan ‘yan mata a makaranta, tare da nuna cewa “ilmantar da mace ita ce ilmantar da Kasa.”